Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 4:7-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Allah kuma ya ce masa, “Mai da hannunka cikin ƙirjinka.” Sai ya mai da hannunsa cikin ƙirjinsa. Sa'ad da ya fitar da shi, ga hannun ya koma kamar sauran jikinsa.

8. Ubangiji kuma ya ce, “Idan kuma ba su gaskata ka ba, ba su kuma kula da mu'ujiza ta fari ba, ya yiwu su gaskata ta biyun.

9. Idan ba su gaskata mu'ujizan nan biyu ba, ba su kuma kula da maganarka ba, sai ka ɗibi ruwa daga Kogin Nilu, ka zuba bisa busasshiyar ƙasa. Ruwan zai zama jini a bisa busasshiyar ƙasa.”

10. Amma Musa ya ce wa Ubangiji, “Ya Ubangijina, ni ba mai lafazi ba ne, ban taɓa zama ba, ko a yanzu ma, bayan da ka yi magana da bawanka, gama ni mai nauyin baki ne, mai nauyin harshe kuma.”

11. Ubangiji kuwa ya ce masa, “Wa ya yi bakin ɗan adam? Wa ya yi bebe ko kurma, ko mai gani ko makaho? Ko ba ni Ubangiji ba ne?

12. Yanzu fa, tafi, zan kasance tare da bakinka, in koya maka abin da za ka faɗa.”

13. Amma Musa ya ce, “Ya Ubangijina, in ka yarda, ka aiki wani.”

14. Ubangiji kuwa ya hasala da Musa, ya ce, “Haruna ɗan'uwanka Balawe ba ya nan ne? Lalle na san shi ya iya magana, ga shi nan ma, yana fitowa ya tarye ka. Sa'ad da ya gan ka kuwa zai yi murna cikin zuciyarsa.

15. Sai ka yi magana da shi. Ka kuma sa masa maganata a baka, zan kuwa kasance tare da bakinka da bakinsa. Zan kuma sanar da ku abin da za ku yi.

16. Shi zai yi maka magana da jama'a, zai zama bakinka, kai kuwa za ka zama kamar Allah a gare shi.

17. Za ka riƙe wannan sanda a hannunka, da shi za ka aikata mu'ujizan.”

18. Musa ya koma wurin Yetro, surukinsa, ya ce masa, “Ina roƙonka, ka bar ni in koma wurin 'yan'uwana a Masar, in ga ko a raye suke har yanzu.”Sai Yetro ya ce wa Musa, “Ka tafi lafiya.”

19. Ubangiji kuwa ya faɗa wa Musa a Madayana, ya koma Masar, gama dukan waɗanda suke neman ransa sun rasu.

20. Saboda haka Musa ya ɗauki matarsa da 'ya'yansa maza, ya haushe su bisa kan jaki, ya koma ƙasar Masar, yana riƙe da sandan Allah a hannunsa.

21. Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “Sa'ad da ka koma Masar, sai ka kula, ka aikata a gaban Fir'auna dukan mu'ujizan da na sa cikin ikonka. Amma zan taurara zuciyarsa, don kada ya bar jama'a su fita.

22. Za ka ce wa Fir'auna, Ubangiji ya ce, ‘Isra'ila ɗan fārina ne.

23. Na ce maka ka bar ɗana ya tafi domin ya bauta mini, amma in ka ƙi ka bar shi ya tafi, yanzu zan kashe ɗan fārinka.”’

24. Ya zama kuwa sa'ad da Musa yake masauki a kan hanya sai Ubangiji ya gamu da shi, ya nema ya kashe shi.

25. Sai Ziffora ta ɗauki ƙanƙara ta yanke loɓar ɗanta, ta taɓa gaban Musa da shi, ta ce, “Kai angon jini kake a gare ni.”

Karanta cikakken babi Fit 4