Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 32:16-33 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Allunan kuwa aikin Allah ne, rubutun kuma na Allah ne da ya zāna a kan allunan.

17. A sa'ad da Joshuwa ya ji hayaniyar jama'ar, sai ya ce wa Musa, “Akwai hargowar yaƙi a zangon.”

18. Musa kuwa ya ce, “Ai, wannan ba hargowar nasara ba ce, ba kuma ta waɗanda yaƙi ya ci ba ce, amma hayaniyar waƙa nake ji.”

19. Yana kusato zango, sai ya ga siffar ɗan maraƙi, mutane na ta rawa. Musa kuwa ya harzuƙa, ya watsar da allunan da suke hannunsa a gindin dutsen, suka farfashe.

20. Ya ɗauki siffar ɗan maraƙin da suka yi, ya ƙone ta, ya niƙe, ta zama gari, ya barbaɗa a ruwa, ya sa Isra'ilawa su sha.

21. Musa ya ce wa Haruna, “Me waɗannan mutane suka yi maka, da ka jawo musu babban zunubi?”

22. Haruna kuwa ya amsa, ya ce, “Ya shugabana, kada ka ji haushina, ka san jama'an nan sarai da irin halinsu na son aikata mugunta.

23. Sun ce mini, ‘Yi mana allahn da zai shugabance mu, gama Musa, mutumin da ya fito da mu daga Masar, ba mu san abin da ya same shi ba.’

24. Ni kuwa sai na ce musu, ‘Bari duk wanda yake da zinariya ya tuɓe.’ Waɗanda suke da ita, suka tuɓe, suka kawo mini, ni kuwa na zuba su cikin wuta, daga nan wannan maraƙi ya fito.”

25. Musa ya ga jama'ar sun sangarce, domin Haruna ya sa su sangarce, ya bar su su bauta wa gunki har suka zama abin kunya a gaban magabtansu.

26. Musa ya tsaya a ƙofar zango, ya ce, “Duk wanda yake wajen Ubangiji ya zo wurina.” Sai Lawiyawa suka tattaru a wurinsa.

27. Ya ce musu, “Ubangiji Allah na Isra'ila ya ce, ‘Kowane mutum ya rataya takobinsa, ya kai ya kawo daga ƙofa zuwa ƙofa cikin zango duka, kowa ya kashe ɗan'uwansa, kowa ya kashe zumunsa, kowa ya kashe maƙwabcinsa.”’

28. Lawiyawa kuwa suka yi yadda Musa ya faɗa. A ranan nan aka kashe mutum wajen talata (3,000).

29. Sai Musa ya ce, “Yau kun ba da kanku ga Ubangiji, gama kowane mutum ya kashe ɗansa da ɗan'uwansa, ta haka kuka jawo wa kanku albarka yau.”

30. Kashegari, Musa ya ce wa mutane, “Kun aikata babban zunubi. Yanzu kuwa zan tafi wurin Ubangiji, watakila zan iya yin kafara domin zunubanku.”

31. Musa ya koma wurin Ubangiji, ya ce, “Kaito, mutanen nan sun aikata zunubi mai girma, sun yi wa kansu gunkin zinariya.

32. Amma ina roƙonka ka gafarta zunubansu, in kuwa ba haka ba, ina roƙonka ka shafe sunana daga cikin littafin da ka rubuta.”

33. Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “Ai, dukan wanda ya yi mini zunubi, shi ne zan shafe sunansa daga cikin littafina.

Karanta cikakken babi Fit 32