Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24
  25. 25
  26. 26
  27. 27
  28. 28
  29. 29
  30. 30
  31. 31
  32. 32
  33. 33
  34. 34
  35. 35
  36. 36
  37. 37
  38. 38
  39. 39
  40. 40

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 32 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Ɗan Maraƙin Zinariya

1. Da mutane suka ga Musa ya yi jinkirin saukowa daga dutsen, sai suka taru wurin Haruna, suka ce masa, “Tashi, ka yi mana allahn da zai shugabance mu, gama ba mu san abin da ya faru da Musa ɗin wanda ya fisshe mu daga ƙasar Masar ba.”

2. Haruna ya ce musu, “Ku tuttuɓe zobban zinariya waɗanda suke kunnuwan matanku, da na 'ya'yanku maza da mata, ku kawo mini.”

3. Sai jama'a duka suka tuttuɓe zobban zinariya da suke a kunnuwansu, suka kawo wa Haruna.

4. Ya karɓi zobban a hannunsu, sai ya narkar da su, ya sassaƙa shi da kurfi, ya siffata ɗan maraƙi. Da jama'a suka gani, sai suka ce, “Allahnku ke nan, ya Isra'ila, wanda ya fisshe ku daga Masar.”

5. Sa'ad da Haruna ya gani, ya gina bagade a gaban siffar maraƙin, ya yi shela, ya ce, “Gobe akwai idi ga Ubangiji.”

6. Kashegari da sassafe, suka tashi, suka miƙa hadayu na ƙonawa da na salama. Jama'ar kuma suka zauna su ci su sha, suka kuma tashi suna rawa.

7. Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Sauka, gama jama'arka da ka fito da su daga ƙasar Masar sun ƙazantar da kansu.

8. Sun yi saurin kaucewa daga hanyar da na umarce su. Sun yi wa kansu ɗan maraƙi na zubi, sun yi masa sujada, sun miƙa masa hadaya, sun kuma ce, ‘Ya Isra'ila, wannan shi ne allahn da ya fisshe ka daga ƙasar Masar.”’

9. Ya kuma ce wa Musa, “Na ga jama'an nan suna da taurinkai.

10. Yanzu dai, ka bar ni kawai fushina ya yi ƙuna a kansu, ya cinye su, amma kai zan maishe ka babbar al'umma.”

11. Amma Musa ya roƙi Ubangiji Allahnsa, ya ce, “Ya Ubangiji, me ya sa ka husata da mutanenka waɗanda ka fisshe su da ƙarfin ikonka mai girma daga ƙasar Masar?

12. Don me za ka sa Masarawa su ce, ‘Ai, don ƙeta ce ya fitar da su, don ya kashe su cikin duwatsu, ya shafe su sarai daga duniya?’ Ka janye zafin fushinka, kada kuma ka jawo wa jama'arka masifa.

13. Ka tuna da bayinka Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, waɗanda kai da kanka ka rantse musu, ka ce, ‘Zan riɓaɓɓanya zuriyarku kamar taurarin sama, in kuma ba ku wannan ƙasa duka da na alkawarta zan bayar ga zuriyarku. Za su kuwa gāje ta har abada.”’

14. Ubangiji kuwa ya huce, ya janye niyyarsa ta jawo masifa a kan jama'arsa.

15. Musa ya sauko daga kan dutsen da allunan dutsen nan biyu na shaida a hannunsa. Allunan rubutattu ne ciki da baya.

16. Allunan kuwa aikin Allah ne, rubutun kuma na Allah ne da ya zāna a kan allunan.

17. A sa'ad da Joshuwa ya ji hayaniyar jama'ar, sai ya ce wa Musa, “Akwai hargowar yaƙi a zangon.”

18. Musa kuwa ya ce, “Ai, wannan ba hargowar nasara ba ce, ba kuma ta waɗanda yaƙi ya ci ba ce, amma hayaniyar waƙa nake ji.”

19. Yana kusato zango, sai ya ga siffar ɗan maraƙi, mutane na ta rawa. Musa kuwa ya harzuƙa, ya watsar da allunan da suke hannunsa a gindin dutsen, suka farfashe.

20. Ya ɗauki siffar ɗan maraƙin da suka yi, ya ƙone ta, ya niƙe, ta zama gari, ya barbaɗa a ruwa, ya sa Isra'ilawa su sha.

21. Musa ya ce wa Haruna, “Me waɗannan mutane suka yi maka, da ka jawo musu babban zunubi?”

22. Haruna kuwa ya amsa, ya ce, “Ya shugabana, kada ka ji haushina, ka san jama'an nan sarai da irin halinsu na son aikata mugunta.

23. Sun ce mini, ‘Yi mana allahn da zai shugabance mu, gama Musa, mutumin da ya fito da mu daga Masar, ba mu san abin da ya same shi ba.’

24. Ni kuwa sai na ce musu, ‘Bari duk wanda yake da zinariya ya tuɓe.’ Waɗanda suke da ita, suka tuɓe, suka kawo mini, ni kuwa na zuba su cikin wuta, daga nan wannan maraƙi ya fito.”

25. Musa ya ga jama'ar sun sangarce, domin Haruna ya sa su sangarce, ya bar su su bauta wa gunki har suka zama abin kunya a gaban magabtansu.

26. Musa ya tsaya a ƙofar zango, ya ce, “Duk wanda yake wajen Ubangiji ya zo wurina.” Sai Lawiyawa suka tattaru a wurinsa.

27. Ya ce musu, “Ubangiji Allah na Isra'ila ya ce, ‘Kowane mutum ya rataya takobinsa, ya kai ya kawo daga ƙofa zuwa ƙofa cikin zango duka, kowa ya kashe ɗan'uwansa, kowa ya kashe zumunsa, kowa ya kashe maƙwabcinsa.”’

28. Lawiyawa kuwa suka yi yadda Musa ya faɗa. A ranan nan aka kashe mutum wajen talata (3,000).

29. Sai Musa ya ce, “Yau kun ba da kanku ga Ubangiji, gama kowane mutum ya kashe ɗansa da ɗan'uwansa, ta haka kuka jawo wa kanku albarka yau.”

30. Kashegari, Musa ya ce wa mutane, “Kun aikata babban zunubi. Yanzu kuwa zan tafi wurin Ubangiji, watakila zan iya yin kafara domin zunubanku.”

31. Musa ya koma wurin Ubangiji, ya ce, “Kaito, mutanen nan sun aikata zunubi mai girma, sun yi wa kansu gunkin zinariya.

32. Amma ina roƙonka ka gafarta zunubansu, in kuwa ba haka ba, ina roƙonka ka shafe sunana daga cikin littafin da ka rubuta.”

33. Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “Ai, dukan wanda ya yi mini zunubi, shi ne zan shafe sunansa daga cikin littafina.

34. Yanzu fa, sai ka tafi, ka bi da mutanen zuwa wurin da zan faɗa maka, ga shi, mala'ikana zai wuce gabanka. Duk da haka a ranar da zan waiwaye ku, zan hukunta su saboda zunubinsu.”

35. Sai Ubangiji ya aika wa mutanen da annoba saboda ɗan maraƙin da suka sa Haruna ya yi musu.