Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 32:11-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Amma Musa ya roƙi Ubangiji Allahnsa, ya ce, “Ya Ubangiji, me ya sa ka husata da mutanenka waɗanda ka fisshe su da ƙarfin ikonka mai girma daga ƙasar Masar?

12. Don me za ka sa Masarawa su ce, ‘Ai, don ƙeta ce ya fitar da su, don ya kashe su cikin duwatsu, ya shafe su sarai daga duniya?’ Ka janye zafin fushinka, kada kuma ka jawo wa jama'arka masifa.

13. Ka tuna da bayinka Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, waɗanda kai da kanka ka rantse musu, ka ce, ‘Zan riɓaɓɓanya zuriyarku kamar taurarin sama, in kuma ba ku wannan ƙasa duka da na alkawarta zan bayar ga zuriyarku. Za su kuwa gāje ta har abada.”’

14. Ubangiji kuwa ya huce, ya janye niyyarsa ta jawo masifa a kan jama'arsa.

15. Musa ya sauko daga kan dutsen da allunan dutsen nan biyu na shaida a hannunsa. Allunan rubutattu ne ciki da baya.

16. Allunan kuwa aikin Allah ne, rubutun kuma na Allah ne da ya zāna a kan allunan.

17. A sa'ad da Joshuwa ya ji hayaniyar jama'ar, sai ya ce wa Musa, “Akwai hargowar yaƙi a zangon.”

18. Musa kuwa ya ce, “Ai, wannan ba hargowar nasara ba ce, ba kuma ta waɗanda yaƙi ya ci ba ce, amma hayaniyar waƙa nake ji.”

19. Yana kusato zango, sai ya ga siffar ɗan maraƙi, mutane na ta rawa. Musa kuwa ya harzuƙa, ya watsar da allunan da suke hannunsa a gindin dutsen, suka farfashe.

20. Ya ɗauki siffar ɗan maraƙin da suka yi, ya ƙone ta, ya niƙe, ta zama gari, ya barbaɗa a ruwa, ya sa Isra'ilawa su sha.

21. Musa ya ce wa Haruna, “Me waɗannan mutane suka yi maka, da ka jawo musu babban zunubi?”

22. Haruna kuwa ya amsa, ya ce, “Ya shugabana, kada ka ji haushina, ka san jama'an nan sarai da irin halinsu na son aikata mugunta.

23. Sun ce mini, ‘Yi mana allahn da zai shugabance mu, gama Musa, mutumin da ya fito da mu daga Masar, ba mu san abin da ya same shi ba.’

24. Ni kuwa sai na ce musu, ‘Bari duk wanda yake da zinariya ya tuɓe.’ Waɗanda suke da ita, suka tuɓe, suka kawo mini, ni kuwa na zuba su cikin wuta, daga nan wannan maraƙi ya fito.”

25. Musa ya ga jama'ar sun sangarce, domin Haruna ya sa su sangarce, ya bar su su bauta wa gunki har suka zama abin kunya a gaban magabtansu.

26. Musa ya tsaya a ƙofar zango, ya ce, “Duk wanda yake wajen Ubangiji ya zo wurina.” Sai Lawiyawa suka tattaru a wurinsa.

Karanta cikakken babi Fit 32