Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 14:8-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Ubangiji ya taurare zuciyar Fir'auna, Sarkin Masar, sai ya bi Isra'ilawa sa'ad da suka fita gabagaɗi.

9. Masarawa kuwa, da dukan dawakan Fir'auna, da karusai, da mahayan dawakansa, da askarawansa, suka bi su, suka ci musu a inda suka yi zango a bakin bahar, kusa da Fi-hahirot wanda ya fuskanci Ba'alzefon.

10. Da Fir'auna ya matso, Isra'ilawa kuwa suka ɗaga idanunsu suka ga Masarawa tafe, sun tasar musu, sai suka firgita ƙwarai, suka yi kuka ga Ubangiji.

11. Suka ce wa Musa, “Donin ba makabarta a Masar, shi ya sa ka fito da mu, mu mutu a jeji? Me ke nan ka yi mana da ka fito da mu daga Masar?

12. Ashe, ba abin da muka faɗa maka tun a Masar ke nan ba cewa, ‘Ka rabu da mu, mu bauta wa Masarawa’? Gama gwamma mu bauta wa Masarawa da mu mutu a jeji.”

13. Sai Musa ya ce wa jama'a, “Kada ku tsorata, ku tsaya cik, ku ga ceton Ubangiji, wanda zai yi muku yau, gama Masarawan nan da kuke gani yau, ba za ku ƙara ganinsu ba faufau.

14. Ubangiji zai yi yaƙi dominku, sai dai ku tsaya kurum!”

15. Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Me ya sa kake yi mini kuka? Faɗa wa Isra'ilawa su ci gaba.

16. Ɗaga sandanka, ka miƙa hannunka a bisa bahar, ka raba shi, domin Isra'ilawa su taka busasshiyar ƙasa cikin bahar, su haye.

17. Ni kuwa zan taurare zukatan Masarawa domin su bi su. Ta haka zan ci nasara bisa Fir'auna da rundunansa, da karusansa, da mahayan dawakansa.

18. Masarawa kuwa za su sani ni ne Ubangiji, sa'ad da na sami nasara bisa kan Fir'auna, da karusansa, da mahayan dawakansa.”

19. Mala'ikan Allah kuwa wanda yake tafiya a gaban rundunar Isra'ila ya tashi ya koma bayansu, haka kuma al'amudin girgijen ya tashi daga gabansu ya tsaya a bayansu.

20. Ya shiga tsakanin sansanin Masarawa da zangon Isra'ilawa. Girgije mai duhu na tsakaninsu, amma ya haskaka wajen Isra'ilawa har gari ya waye, ba wanda ya kusaci wani.

Karanta cikakken babi Fit 14