Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24
  25. 25
  26. 26
  27. 27
  28. 28
  29. 29
  30. 30
  31. 31
  32. 32
  33. 33
  34. 34
  35. 35
  36. 36
  37. 37
  38. 38
  39. 39
  40. 40

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Hayen Bahar Maliya

1. Ubangiji ya ce wa Musa,

2. “Faɗa wa Isra'ilawa su juya su yi zango a gaban Fi-hahirot tsakanin Migdol da bahar, a gaban Ba'alzefon. Sai ku yi zango gab da bahar.

3. Gama Fir'auna zai ce, ‘Aha, Isra'ilawa sun rikice cikin ƙasar, hamada kuwa ta cinye su.’

4. Zan taurare zuciyar Fir'auna, zai kuwa bi ku, ni Ubangiji zan nuna ɗaukakata a bisa Fir'auna da dukan rundunansa. Masarawa kuwa za su sani ni ne Ubangiji.” Haka kuwa Isra'ilawa suka yi.

5. Da aka faɗa wa Sarkin Masar jama'a sun gudu, sai shi da fādawansa suka sāke tunaninsu game da jama'ar, suka ce, “Me muka yi ke nan, da muka bar Isra'ilawa su fita daga cikin bautarmu?”

6. Ya kuwa shirya karusarsa, ya ɗauki rundunarsa tare da shi.

7. Ya kuma ɗauki zaɓaɓɓun karusai ɗari shida da sauran karusan Masar duka waɗanda shugabanni suke bi da su.

8. Ubangiji ya taurare zuciyar Fir'auna, Sarkin Masar, sai ya bi Isra'ilawa sa'ad da suka fita gabagaɗi.

9. Masarawa kuwa, da dukan dawakan Fir'auna, da karusai, da mahayan dawakansa, da askarawansa, suka bi su, suka ci musu a inda suka yi zango a bakin bahar, kusa da Fi-hahirot wanda ya fuskanci Ba'alzefon.

10. Da Fir'auna ya matso, Isra'ilawa kuwa suka ɗaga idanunsu suka ga Masarawa tafe, sun tasar musu, sai suka firgita ƙwarai, suka yi kuka ga Ubangiji.

11. Suka ce wa Musa, “Donin ba makabarta a Masar, shi ya sa ka fito da mu, mu mutu a jeji? Me ke nan ka yi mana da ka fito da mu daga Masar?

12. Ashe, ba abin da muka faɗa maka tun a Masar ke nan ba cewa, ‘Ka rabu da mu, mu bauta wa Masarawa’? Gama gwamma mu bauta wa Masarawa da mu mutu a jeji.”

13. Sai Musa ya ce wa jama'a, “Kada ku tsorata, ku tsaya cik, ku ga ceton Ubangiji, wanda zai yi muku yau, gama Masarawan nan da kuke gani yau, ba za ku ƙara ganinsu ba faufau.

14. Ubangiji zai yi yaƙi dominku, sai dai ku tsaya kurum!”

15. Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Me ya sa kake yi mini kuka? Faɗa wa Isra'ilawa su ci gaba.

16. Ɗaga sandanka, ka miƙa hannunka a bisa bahar, ka raba shi, domin Isra'ilawa su taka busasshiyar ƙasa cikin bahar, su haye.

17. Ni kuwa zan taurare zukatan Masarawa domin su bi su. Ta haka zan ci nasara bisa Fir'auna da rundunansa, da karusansa, da mahayan dawakansa.

18. Masarawa kuwa za su sani ni ne Ubangiji, sa'ad da na sami nasara bisa kan Fir'auna, da karusansa, da mahayan dawakansa.”

19. Mala'ikan Allah kuwa wanda yake tafiya a gaban rundunar Isra'ila ya tashi ya koma bayansu, haka kuma al'amudin girgijen ya tashi daga gabansu ya tsaya a bayansu.

20. Ya shiga tsakanin sansanin Masarawa da zangon Isra'ilawa. Girgije mai duhu na tsakaninsu, amma ya haskaka wajen Isra'ilawa har gari ya waye, ba wanda ya kusaci wani.

21. Da Musa ya miƙa hannunsa bisa bahar, sai Ubangiji ya sa iskar gabas mai ƙarfi ta tsaga bahar, ta tura ta baya, ta yi ta hurawa dukan dare har bahar ta bushe, ruwan kuwa ya dāre.

22. Isra'ilawa kuwa suka bi ta tsakiyar bahar, a busasshiyar ƙasa. Ruwan ya zama musu katanga dama da hagu.

23. Masarawa kuwa suka bi su har tsakiyar bahar, da dawakan Fir'auna duka, da karusansa, da mahayan dawakansa.

24. Da asubahin fāri, Ubangiji, daga cikin al'amudin wuta da na girgije, ya duba rundunar Masarawa, ya gigitar da su.

25. Kafafun karusansu suka fara kwaɓewa, da ƙyar ake jansu. Daga nan Masarawa suka ce, “Mu guje wa Isra'ilawa, gama Ubangiji yana yaƙi dominsu gāba da Masarawa.”

26. Sa'an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Miƙa hannunka bisa bahar domin ruwa ya koma bisa kan Masarawa, da bisa karusansu, da mahayan dawakansu.”

27. Gari na wayewa sai Musa ya miƙa hannunsa bisa bahar, ruwan kuwa ya koma kamar yadda yake a dā. Da Masarawa suka yi ƙoƙarin tserewa, sai ruwan ya rufe su. Ubangiji kuwa ya hallaka su a tsakiyar bahar.

28. Ruwan ya komo ya rufe dukan karusai, da mahayan dawakai, da dukan rundunar Fir'auna waɗanda suka bi ta cikin bahar, ba ko ɗaya da ya ragu.

29. Amma Isra'ilawa suka yi tafiya a busasshiyar ƙasa a tsakiyar bahar, ruwa kuwa ya yi musu katanga dama da hagu.

30. A wannan rana, Ubangiji ya ceci Isra'ilawa daga hannun Masarawa. Isra'ilawa kuwa suka ga gawawwakin Masarawa a bakin bahar.

31. Isra'ilawa suka ga gawurtaccen aikin da Ubangiji ya yi gāba da Masarawa. Isra'ilawa kuwa suka ji tsoron Ubangiji, suka gaskata Ubangiji da bawansa Musa.