Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 14:18-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Masarawa kuwa za su sani ni ne Ubangiji, sa'ad da na sami nasara bisa kan Fir'auna, da karusansa, da mahayan dawakansa.”

19. Mala'ikan Allah kuwa wanda yake tafiya a gaban rundunar Isra'ila ya tashi ya koma bayansu, haka kuma al'amudin girgijen ya tashi daga gabansu ya tsaya a bayansu.

20. Ya shiga tsakanin sansanin Masarawa da zangon Isra'ilawa. Girgije mai duhu na tsakaninsu, amma ya haskaka wajen Isra'ilawa har gari ya waye, ba wanda ya kusaci wani.

21. Da Musa ya miƙa hannunsa bisa bahar, sai Ubangiji ya sa iskar gabas mai ƙarfi ta tsaga bahar, ta tura ta baya, ta yi ta hurawa dukan dare har bahar ta bushe, ruwan kuwa ya dāre.

22. Isra'ilawa kuwa suka bi ta tsakiyar bahar, a busasshiyar ƙasa. Ruwan ya zama musu katanga dama da hagu.

23. Masarawa kuwa suka bi su har tsakiyar bahar, da dawakan Fir'auna duka, da karusansa, da mahayan dawakansa.

24. Da asubahin fāri, Ubangiji, daga cikin al'amudin wuta da na girgije, ya duba rundunar Masarawa, ya gigitar da su.

25. Kafafun karusansu suka fara kwaɓewa, da ƙyar ake jansu. Daga nan Masarawa suka ce, “Mu guje wa Isra'ilawa, gama Ubangiji yana yaƙi dominsu gāba da Masarawa.”

26. Sa'an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Miƙa hannunka bisa bahar domin ruwa ya koma bisa kan Masarawa, da bisa karusansu, da mahayan dawakansu.”

27. Gari na wayewa sai Musa ya miƙa hannunsa bisa bahar, ruwan kuwa ya koma kamar yadda yake a dā. Da Masarawa suka yi ƙoƙarin tserewa, sai ruwan ya rufe su. Ubangiji kuwa ya hallaka su a tsakiyar bahar.

28. Ruwan ya komo ya rufe dukan karusai, da mahayan dawakai, da dukan rundunar Fir'auna waɗanda suka bi ta cikin bahar, ba ko ɗaya da ya ragu.

29. Amma Isra'ilawa suka yi tafiya a busasshiyar ƙasa a tsakiyar bahar, ruwa kuwa ya yi musu katanga dama da hagu.

30. A wannan rana, Ubangiji ya ceci Isra'ilawa daga hannun Masarawa. Isra'ilawa kuwa suka ga gawawwakin Masarawa a bakin bahar.

31. Isra'ilawa suka ga gawurtaccen aikin da Ubangiji ya yi gāba da Masarawa. Isra'ilawa kuwa suka ji tsoron Ubangiji, suka gaskata Ubangiji da bawansa Musa.

Karanta cikakken babi Fit 14