Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 47:18-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Sa'ad da wannan shekara ta ƙare, sai suka zo wurinsa a shekara ta biyu, suka ce masa, “Ranka ya daɗe. Ba za mu ɓoye wa shugabanmu ba cewa kuɗinmu duka mun kashe, garkunan dabbobin kuma sun zama naka. Banda jikunanmu da gonakunmu, ba kuwa abin da ya rage mana.

19. Kada ka bar mu mu mutu, ka yi wata dabara! Kada ka bari mu rasa gonakinmu. Ka musaye mu da abinci, mu da gonakunmu. Mu kuwa za mu zama bayin Fir'auna, ka kuma ba mu iri domin mu rayu, kada mu mutu don kuma kada ƙasar ta zama kango.”

20. Ta haka Yusufu ya saya wa Fir'auna ƙasar Masar duka, gama Masarawa duka sun sayar da saurukansu, saboda yunwa ta tsananta musu. Ƙasar ta zama halaliyar Fir'auna.

21. Yusufu ya mai da jama'ar bayi daga wannan kan iyaka na Masar zuwa wancan.

22. Sai gonakin firistoci ne kaɗai bai saya ba, gama firistocin suna da rabo wanda Fir'auna ya yanka musu, da rabon da Fir'auna yake ba su suke zaman gari, sabili da haka ba su sayar da gonakinsu ba.

23. Yusufu ya ce wa jama'ar, “Ga shi, a yau na saya wa Fir'auna ku da gonakinku. Yanzu fa, ga iri dominku, za ku shuka gonakin.

24. Da haka za ku ba da kashi ɗaya cikin biyar ga Fir'auna, kashi huɗu cikin biyar kuwa ya zama naku din iri na shuka a gonakinku, don kuma abincinku, da na iyalan gidanku, da na 'yan ƙanananku.”

25. Suka ce, “Ka ceci rayukanmu, in ko ya gamshe ka, ya shugaba, mā zama bayin Fir'auna.”

26. Sai Yusufu ya kafa doka daga wannan rana har wa yau game da ƙasar Masar wadda ta ce, Fir'auna zai sami kashi ɗaya daga cikin biyar, sai dai gonakin firistoci kaɗai ne ba su zama na Fir'auna ba.

27. Ta haka fa Isra'ila ya yi zamansa a ƙasar Masar a ƙasar Goshen, suka kuwa sami mahalli a cikinta suka hayayyafa suka riɓaɓɓanya ƙwarai.

28. Yakubu kuma ya zauna a ƙasar Masar shekara goma sha bakwai, don haka kwanakin Yakubu, wato shekarun ransa, shekara ce ɗari da arba'in da bakwai.

29. A sa'ad da lokaci ya gabato da Isra'ila zai mutu, ya kira ɗansa Yusufu ya ce masa, “Idan zan sami tagomashi a idonka, ka sa hannunka a ƙarƙashin cinyata, ka ɗau alkawari za ka aikata mini aminci da gaskiya. Kada ka binne ni a Masar,

30. amma bari in kwanta tare da kakannina, ka ɗauke ni daga Masar, ka binne ni a makabartarsu.”Ya amsa ya ce, “Zan aikata yadda ka faɗa.”

31. Sai Yakubu ya ce, “Rantse mini.” Sai Yusufu ya rantse masa. Sa'an nan sai Isra'ila ya mai da kai bisa kan gadonsa.

Karanta cikakken babi Far 47