Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 44:22-32 Littafi Mai Tsarki (HAU)

22. Ranka ya daɗe, muka kuwa ce, ‘Saurayin ba zai iya rabuwa da mahaifinsa ba, gama in ya rabu da mahaifinsa, mahaifinsa zai mutu.’

23. Sai ka amsa wa barorinka, ka ce, ‘In ba autanku ya zo tare da ku ba, ba za ku ƙara ganin fuskata ba.’

24. “Sa'ad da muka koma a wurin baranka, mahaifinmu, muka mayar masa da dukan abin da ka ce.

25. Don haka sa'ad da mahaifinmu ya ce, ‘Koma, ku sayo mana ɗan abinci,’

26. sai muka ce, ‘Ba za mu iya gangarawa ba, amma idan autanmu zai tafi tare da mu, za mu gangara, gama ba dama mu ga fuskar mutumin sai ko autanmu yana tare da mu.’

27. Sa'an nan baranka, mahaifinmu, ya ce mana, ‘Kun sani 'ya'ya biyu matata ta haifa mini,

28. ɗayan ya bar ni, na kuwa ɗauka, hakika an yayyage shi kaca kaca, gama ban ƙara ganinsa ba.

29. In kuka ɗauke wannan kuma daga gare ni, mai yiwuwa ne a kashe shi, to, za ku sa baƙin ciki ya ishe ni, da tsufana, har ya kashe ni.’

30-31. “Domin haka kuwa, yanzu, idan na koma wurin baranka, mahaifina, ba tare da saurayin ba, in har bai ga yaron tare da ni ba, zai mutu, gama ransa ya shaƙu da saurayin, barorinka kuwa za su sa baranka, mahaifinmu, ya mutu cikin baƙin ciki, da tsufansa.

32. Gama ni baranka na ɗauki lamunin saurayin wurin mahaifinsa da cewa, ‘In ban komo maka da shi ba, sai alhakinsa ya zauna a kaina a gaban mahaifina duka raina.’

Karanta cikakken babi Far 44