Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 27:21-36 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Ishaku kuwa ya ce wa Yakubu, “Matso kusa in ka yarda, don in lallaluba ka, ɗana, domin in hakikance ko kai ne ɗana Isuwa, ko babu.”

22. Saboda haka Yakubu ya matsa kusa da Ishaku mahaifinsa, sai ya lallaluba shi, ya ce, “Murya, muryar Yakubu ce, amma hannuwa, hannuwan Isuwa ne.”

23. Amma bai gane shi ba, gama hannuwansa gargasa ne kamar hannuwan ɗan'uwansa Isuwa, saboda haka ya sa masa albarka.

24. Ya ce, “Hakika, kai ne ɗana Isuwa?”Ya amsa, “Ni ne.”

25. Ya ce, “Kawo mini naman da ka harbo, in ci in sa maka albarka.” Sai ya kawo masa, ya kuwa ci, ya kawo masa ruwan inabi, ya sha.

26. Mahaifinsa Ishaku kuwa ya ce masa, “Zo kusa ka sumbace ni, ɗana.”

27. Don haka ya zo kusa ya sumbace shi. Ishaku ya sansana rigunansa, ya sa masa albarka, ya ce,“Duba, ƙanshin ɗanaYana kama da ƙanshin jejiWanda Ubangiji ya sa wa albarka!

28. Allah ya ba ka daga cikin raɓarsama,Daga cikin ni'imar ƙasa,Da hatsi a yalwace da ruwan inabi.

29. Bari jama'a su bauta maka,Al'ummai kuma su sunkuya maka.Za ka yi shugabancin 'yan'uwanka,Allah ya sa 'ya'yan mahaifiyarka susunkuya maka.La'ananne ne dukan wanda yala'anta ka,Albarkatacce ne dukan wanda ya samaka albarka.”

30. Ishaku yana gama sa wa Yakubu albarka, Yakubu yana fita daga gaban mahaifinsa ke nan sai ga Isuwa ɗan'uwansa ya komo daga farauta.

31. Shi kuma ya shirya abinci mai daɗin ci, ya kawo wa mahaifinsa. Sai ya ce wa mahaifinsa, “In ka yarda baba, ka tashi, ka ci naman da na harbo don ka sa mini albarka.”

32. Mahaifinsa Ishaku ya ce masa, “Wane ne kai?”Ya amsa, “Ni ne ɗanka, ɗan farinka, Isuwa.”

33. Ishaku kuwa ya yi makyarkyata ƙwarai, ya ce, “Wane ne wannan fa, da ya farauto naman ya kawo mini, na kuwa cinye kafin ka zo, har na sa masa albarka? – i, albarkatacce zai zama.”

34. Da Isuwa ya ji kalmomin mahaifinsa, sai ya yi kūwwa da kuka mai tsananin gaske, ya ce wa mahaifinsa, “Ka sa mini albarka, har da ni ma, ya babana.”

35. Amma ya ce, “Ɗan'uwanka ya zo cikin makirci, ya karɓe albarkarka.”

36. Isuwa ya ce, “Ba saboda haka ne aka raɗa masa suna Yakubu ba? Gama sau biyu ke nan yake yi mini ƙwace. Ya ƙwace mini matsayina na ɗan fari, ga shi kuma, yanzu ya ƙwace mini albarkata.” Sa'an nan ya ce, “Ba sauran albarkar da ka rage mini?”

Karanta cikakken babi Far 27