Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ezra 6:15-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. An gama ginin Haikali a ran ashirin da uku ga watan Adar, a shekara ta shida ta sarautar sarki Dariyus.

16. Sai mutanen Isra'ila, da firistoci, da Lawiyawa, da sauran waɗanda suka komo daga bauta, suka yi bikin keɓe Haikalin Allah da murna.

17. A bikin keɓe Haikalin Allah, suka miƙa bijimai ɗari, da raguna ɗari biyu,da 'yan raguna ɗari huɗu. Suka kuma miƙa hadayu don zunubi saboda dukan Isra'ila, bunsurai goma sha biyu, bisa ga yawan kabilan Isra'ila.

18. Sai suka karkasa firistoci da Lawiyawa ƙungiya domin yin aikin Ubangiji a Urushalima kamar yadda aka rubuta a Attaura ta Musa.

19. A rana ta goma sha huɗu ga watan fari, sai waɗanda suka komo daga bauta suka kiyaye Idin Ƙetarewa.

20. Gama firistoci da Lawiyawa sun tsarkake kansu, suka kuwa tsarkaka, sai suka yanka ragon Idin Ƙetarewa saboda dukan waɗanda suka komo daga bauta, da kuma saboda 'yan'uwansu firistoci, da su kansu.

21. Mutanen Isra'ila waɗanda suka komo daga zaman talala suka ci tare da kowane mutumin da ya haɗa kai da su, ya kuma keɓe kansa daga ƙazantar al'umman ƙasar, domin ya bi Ubangiji Allah na Isra'ila.

22. Suka kuma kiyaye idin abinci marar yisti kwana bakwai da murna, gama Ubangiji ya sa su yi murna, ya kuma juyo da zuciyar Sarkin Assuriya wajensu, saboda haka ya taimake su da aikin Haikalin Allah, Allah na Isra'ila.

Karanta cikakken babi Ezra 6