Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ezra 3:10-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Sa'ad da maginan suka aza harsashin ginin Haikalin Ubangiji, firistoci suna nan tsaye saye da rigunansu, suna riƙe da ƙahoni, Lawiyawa kuma 'ya'yan Asaf, suna riƙe da kuge domin su yabi Ubangiji, bisa ga umarnin Dawuda, Sarkin Isra'ila.

11. Da bangirma suka raira waƙa ta yabo da godiya ga ubangiji, suna cewa,“Ubangiji nagari ne,Gama ƙaunarsa marar matuƙa ce,Ta tabbata har abada ga Isra'ila.”Sai mutane duka suka ɗaga murya da ƙarfi suka yabi Ubangiji, saboda an aza harsashin ginin Haikalin Ubangiji.

12. Amma da yawa daga cikin firistoci, da Lawiyawa, da shugabannin gidajen kakanni, wato tsofaffi waɗanda suka ga Haikali na farko, suka yi kuka da babbar murya a sa'ad da suka ga an aza harsashin ginin wannan Haikali. Waɗansu kuwa suka yi sowa don farin ciki.

13. Saboda haka mutane ba su iya rarrabe amon muryar murna da ta kuka ba, gama mutanen suka ɗaga murya da ƙarfi har aka ji su daga nesa.

Karanta cikakken babi Ezra 3