Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 5:7-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Domin haka ni na ce, ‘Da yake kin cika rikici fiye da sauran ƙasashen da suke kewaye da suke, kin ƙi yin tafiya cikin dokokina, ba ki kiyaye ka'idodin ba, amma kin bi ka'ikodin al'umman da take kewaye da ke,

8. to, ina gāba da ke, zan hukunta ki a idanun al'ummai.

9. Saboda yawan abubuwa masu banƙyama da kika aikata, zan yi miki abin da ban taɓa yi ba, ba kuwa zan sāke yin irinsa ba.

10. Ubanni za su cinye 'ya'yansu, 'ya'ya kuma za su cinye ubanninsu. Zan hukunta ki, waɗanda kuma suka tsira zan watsar da su ko'ina.

11. “‘Tun da yake kin ƙazantar da Haikalina mai tsarki da gumakanki da abubuwanki masu banƙyama, hakika, ni Ubangiji Allah, zan kawar da ke, ba zan ji tausayinki ba, ba kuwa zan haƙura ba.

12. Sulusinki zai mutu da annoba da yunwa. Takobi kuma zai kashe sulusinki, sa'an nan zan watsar da sulusinki ko'ina, zan kuma zare takobi a kansu.

13. “‘Ta haka zan sa fushina ya huce, hasalata kuma a kansu ta lafa, ni kuma in wartsake. Sa'an nan za su sani ni Ubangiji na yi magana da zafin kishi sa'ad da na iyar da fushina a kansu.

14. Zan kuma maishe ki kufai da abin zargi ga al'ummai da suke kewaye da ke, da kuma a idanun dukan masu wucewa.

15. “‘Za ki zama abin zargi, da abin ba'a, da abin faɗaka, da abin tsoro ga al'ummai da suke kewaye da ke sa'ad da na hukunta ki da zarin fushina, ni Ubangiji na faɗa.

16. Gama zan aiko miki da masifu na yunwa domin hallakarwa. Zan aiko miki da su don su hallaka ki. Zan kawo miki yunwa mai tsanani, in sa abincinki ya ƙare.

17. Zan aiko miki da yunwa da namomin jeji, za su washe 'ya'yanki. Annoba da zub da jini za su ratsa cikinki. Zan kuma kawo takobi a kanki, ni Ubangiji na faɗa.”’

Karanta cikakken babi Ez 5