Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 46:13-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. “Kowace safiya za a yi hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji da ɗan rago bana ɗaya marar lahani.

14. Tare da hadaya ta ƙonawa, za a ba da wajen ɗaya bisa shida na garwar gari, da kwalaba biyu na man zaitun don cuɗa gari, domin a yi hadaya ga Ubangiji. Wannan ita ce ka'idar hadaya ta ƙonawa ta yau da kullum.

15. Za a ba da ɗan rago, da gari, da mai, kowace safiya domin yin hadaya ta ƙonawa.

16. “Ni Ubangiji Allah na ce, idan sarki ya yi wa wani daga cikin 'ya'yansa kyauta daga cikin gādonsa, sai kyautar ta zama ta 'ya'yansa, dukiyarsu ce ta gādo.

17. Amma idan sarki ya yi wa wani daga cikin barorinsa kyauta daga cikin gādonsa, kyautar za ta zama tasa har shekarar 'yantarwa, sa'an nan kyautar za ta koma a hannun sarki. 'Ya'yansa maza ne kaɗai za su riƙe kyauta daga cikin gādonsa din din din.

18. Kada sarki ya ƙwace rabon gādon jama'a, ya hana musu. Sai ya ba 'ya'yansa maza rabon gādo daga cikin abin da yake nasa, amma kada ya ƙwace wa jama'ata abin da suka mallaka har su warwatse.”

19. Sai mutumin ya bi da ni ta hanyar da take gefen ƙofa mai fuskantar arewa, wajen jerin tsarkakakkun ɗakuna na firistoci, waɗanda suke fuskantar arewa. Na kuma ga wani wuri daga can ƙurewar yamma.

20. Sai ya ce mini, “Wannan shi ne wurin da firistoci za su dafa hadaya domin laifi, da hadaya domin zunubi, a nan ne kuma za su toya hadaya ta gāri, domin kada su kai su a filin waje, su sa wa mutane tsarki.”

21. Ya kuma kai ni a farfajiyar waje, ya bi da ni zuwa kusurwa huɗu na farfajiya. Akwai ɗan fili a kowace kusurwa.

22. Girman kowane ɗan fili tsawonsa kamu arba'in ne, faɗin kuma kamu talatin.

23. A cikin kowane ɗan fili na kusurwa huɗu ɗin akwai jerin duwatsu. Aka gina murhu ƙarƙashin jerin duwatsun.

24. Sa'an nan ya ce mini, “Waɗannan su ne ɗakunan dahuwa inda masu hidima a Haikali za su dafa hadayun da jama'a suka kawo.”

Karanta cikakken babi Ez 46