Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 46:1-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “Ni Ubangiji Allah na ce za a rufe ƙofar fili ta can ciki wadda take fuskantar gabas dukan ranaku shida na aiki, amma za a buɗe ta a ranar Asabar da a amaryar wata.

2. Sarki zai shiga ta ƙofar shirayi daga waje, sa'an nan ya tsaya kusa da ginshiƙin ƙofar. Sai firistoci su miƙa hadayarsa ta ƙonawa, da hadayunsa na salama, shi kuwa ya yi sujada s bakin ƙofar, sa'an nan ya fita, amma ba za a rufe ƙofar ba sai da maraice.

3. Jama'ar ƙasar za su yi wa Ubangiji sujada a bakin wannan ƙofa a ranakun Asabar da a amaryar wata.

4. Hadaya ta ƙonawa da sarki zai miƙa wa Ubangiji a ranar Asabar 'yan raguna shida ne da rago ɗaya marasa lahani.

5. Gārin hadaya da za a yi tare da rago wajen garwa guda ne. Wanda za a yi tare da 'yan raguna kuwa zai zama gwargwadon ƙarfinsa. Zai ba da mai wajen kwalaba shida domin kowace garwa ta gari.

6. A amaryar wata kuwa zai miƙa bijimi, da 'yan raguna shida, da rago, dukansu marasa lahani.

7. Gārin hadayar da za a yi tare da bijimin wajen garwa guda ne, haka kuma gari na wadda za a yi tare da ragon, da gari na wadda za a yi tare da 'yan raguna kuma, zai zama gwargwadon ƙarfinsa. Zai ba da man zaitun wajen kwalaba shida domin kowace garwa ta garin.

8. Sa'ad da sarki zai shiga, sai ya shiga ta ƙofar shirayin, ya kuma fita ta nan.

9. “Sa'ad da jama'ar ƙasar sun zo yi wa Ubangiji sujada a lokatan ƙayyadaddun idodi, wanda ya shiga ta ƙofar arewa, sai ya fita ta ƙofar kudu. Wanda kuma ya shiga ta ƙofar kudu, sai ya fita ta ƙofar arewa. Kada kowa ya fita ta ƙofar da ya shiga, amma sai kowa ya fita ta akasin ƙofar da ya shiga.

10. Sa'ad da suka shiga, sai sarki ya shiga tare da su, sa'ad da suka fita kuma, sai ya fita.

11. A lokacin idodi da ƙayyadaddun lokatai, gārin hadayar da za a yi tare da bijimi wajen garwa guda ne, haka kuma na wadda za a yi tare da ragon, na wadda za a yi tare da 'yan ragunan kuwa, sai mutum ya kawo gwargwadon ƙarfinsa. A kuma kawo wajen kwalaba shida na man zaitun domin kowace garwa ta gari.

12. “Sa'ad da sarki ya kawo hadayar ƙonawa ko hadayar salama ta yardar rai ga Ubangiji, sai a buɗe masa ƙofar da take fuskantar gabas. Zai kuwa miƙa hadayarsa ta ƙonawa ko ta salama kamar yadda yakan yi a ranar Asabar. Bayan da ya fita, sai a rufe ƙofa.

13. “Kowace safiya za a yi hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji da ɗan rago bana ɗaya marar lahani.

14. Tare da hadaya ta ƙonawa, za a ba da wajen ɗaya bisa shida na garwar gari, da kwalaba biyu na man zaitun don cuɗa gari, domin a yi hadaya ga Ubangiji. Wannan ita ce ka'idar hadaya ta ƙonawa ta yau da kullum.

Karanta cikakken babi Ez 46