Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 45:15-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Za ku ba da tunkiya ɗaya daga kowane garke mai tumaki ɗari biyu, a cikin Isra'ila.“Waɗannan su ne hadayu na gari, da na ƙonawa, da na salama, domin a yi musu kafara, ni Ubangiji Allah na faɗa.

16. “Dukan mutanen ƙasar za su yi wannan bayarwar domin Sarkin Isra'ila.

17. Sarki ne da nawayar ba da hadayun ƙonawa, da na gari, da na sha a lokacin idodi da na amaryar wata, da ranakun Asabar, da lokacin dukan ƙayyadaddun idodin mutanen Isra'ila. Zai kuma ba da hadayu don zunubi da na salama domin a yi wa mutanen Isra'ila kafara.”

18. “Ni Ubangiji Allah na ce, rana ta fari ga watan fari, za ku ɗauki bijimi marar lahani don a tsarkake Haikalin.

19. Firist zai ɗibi jinin hadaya domin zunubi ya shafa shi a madogaran ƙofar Haikalin, da kusurwa huɗu na dakalin bagaden, da ginshiƙan ƙofar fili na can ciki.

20. Za ku yi haka kuma a rana ta bakwai ga watan, saboda wanda ya yi laifi da kuskure, ko da rashin sani. Ta haka ne za ku yi wa Haikalin kafara.

21. “A kan rana ta goma sha huɗu ga watan fari kuma za ku kiyaye Idin Ƙetarewa. Za ku riƙa cin abinci marar yisti har kwana bakwai.

22. A ranar, sarki zai ba da bijimi domin kansa da jama'ar ƙasar, saboda yin hadaya don zunubi.

23. A ranaku bakwai na Idin, zai ba da bijimi bakwai da raguna bakwai marasa lahani hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. Kowace rana kuma zai ba da bunsuru hadaya don zunubi.

24. Zai kuma ba da hadaya ta gari, mudu guda domin kowane bijimi, da mudu guda domin kowane rago, da wajen kwalaba shida na mai tare da kowane mudu.

25. “A rana ta goma sha biyar ga watan bakwai, zai kuma ba da abubuwan nan har kwana bakwai domin yin hadaya don zunubi, da hadaya ta ƙonawa, da hadaya ta gari game da mai.”

Karanta cikakken babi Ez 45