Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 43:4-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Zatin Ubangiji ya shiga Haikalin ta ƙofar gabas.

5. Ruhu kuwa ya ɗaga ni, ya kai ni a farfajiya ta can ciki, sai ga zatin Ubangiji ya cika Haikali.

6. Sa'ad da mutumin yake tsaye kusa da ni, sai Ubangiji ya yi magana da ni daga cikin Haikalin.

7. Ya ce mini, “Ɗan mutum, wannan wuri shi ne kursiyin sarautata da kilisaina, inda zan zauna tsakiyar mutanen Isra'ila har abada. Mutanen Isra'ila da sarakunansu ba za su ƙara ɓata sunana mai tsarki ta wurin bauta wa gumaka da gina siffofin sarakunansu da suka mutu ba,

8. ko kuwa ta wurin sa dokin ƙofarsu kusa da dokin ƙofata, da kuma ta kafa madogaran ƙofarsu kusa da nawa, sai dai katangar da ta yi mana tsakani. Sun ɓata sunana mai tsarki da ayyukansu masu banƙyama, don haka na hallaka su saboda sun sa na husata.

9. Yanzu sai su zubar da gumakansu da siffofin sarakunansu nesa da ni, ni kuwa zan zauna a cikinsu har abada.

Karanta cikakken babi Ez 43