Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 41:5-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Sai kuma ya auna bangon Haikalin, kaurinsa kamu shida ne. Faɗin ɗakunan da suke kewaye da Haikalin kamu huɗu ne.

6. Ɗakunan benaye ne masu hawa uku. Akwai ɗakuna talatin a kowane hawa. Akwai katanga kewaye da Haikalin don ta tokare ɗakunan, domin ba a so ɗakunan su jingina da bangon Haikalin.

7. Faɗin ɗakunan yana ƙaruwa daga hawa zuwa hawa, gama katangar da take kewaye da Haikali ta yi ta ƙaruwa daga hawa zuwa hawa. A gefen Haikalin akwai matakan hawa. Don haka ana iya hawa daga ɗaki na ƙasa zuwa hawa na uku ta hanyar hawa na biyu.

8. Na ga harsashi mai faɗi kewaye da Haikalin. Tsawon harsashin gini na ɗakunan karan awo mai tsawon kamu shida ne.

9-10. Kaurin katangar waje ta ɗakunan kamu biyar ne. Faɗin filin da yake tsakanin ɗakunan waje da na Haikali kamu ashirin ne kewaye da Haikalin.

11. Ana buɗe ƙofofin ɗakuna a wajen filin da yake tsakanin ɗakuna. Ƙofa ɗaya tana fuskantar wajen arewa, ɗaya kuma tana fuskantar wajen kudu. Faɗin filin da ya ragu kamu biyar ne.

12. Ginin da yake fuskantar farfajiyar Haikali a wajen yamma, faɗinsa kamu saba'in ne. Kaurin ginin kamu biyar ne, tsawonsa kuma kamu tasa'in ne.

13. Sai ya auna Haikalin, tsawonsa kamu ɗari. Tsawon farfajiyar, da ginin, da katangarsa, kamu ɗari.

14. Faɗin Haikalin da farfajiyar a fuskar gabas, kamu ɗari.

15-16. Ya kuma auna tsawon ginin da yake fuskantar farfajiyar da take wajen yamma da hanyar fita, kamu ɗari ne. Cikin Haikalin, da ɗaki na can ciki, da shirayi, dukansu uku suna da tagogi masu gagara badau. An manne bangon Haikalin da yake fuskantar shirayin da katako, tun daga ƙasa har zuwa tagogi. [Tagogin kuma an rufe su.]

17-18. An zana siffofin kerubobi da na itatuwan dabino a bangon Haikali ciki da waje har zuwa kan ƙofar shiga. Zanen siffar itacen dabino yana a tsakanin kerub da kerub. Kowane kerub yana da fuska biyu.

19. Fuska ɗaya kamar ta mutum tana fuskantar zānen siffar itacen dabino a wannan gefe. Ɗaya fuskar kamar ta sagarin zaki tana fuskantar zānen siffar itacen dabino na wancan gefe. Haka aka zana dukan jikin bangon Haikalin da su.

Karanta cikakken babi Ez 41