Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 39:2-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Zan juya ka in sa ka gaba in tashi daga ƙurewar arewa, in kawo ka don ka fāɗa wa duwatsun Isra'ila.

3. Sa'an nan zan karya bakan da yake a hannun hagunka, in sa kiban da suke a hannun damanka su fāɗi.

4. Za ka fāɗi matacce a kan duwatsun Isra'ila, kai da dukan rundunanka, da jama'ar da suke tare da kai. Zan ba da gawawwakinka ga tsuntsaye da dabbobi masu cin nama.

5. Za ka mutu a filin saura, gama haka ni Ubangiji Allah na faɗa.’

6. Zan aika da wuta a kan Magog, da a kan waɗanda suke zaman lafiya a ƙasashen gāɓar teku, za su kuwa sani ni ne Ubangiji.

7. Zan sanar da sunana mai tsarki a tsakiyar jama'ata, wato Isra'ila, ba zan ƙara bari a ɓata sunana mai tsarki ba, al'ummai kuwa za su sani ni ne Ubangiji Mai Tsarki a cikin Isra'ila.

8. “Ga shi, ranar da na ambata tana zuwa, hakika kuwa tana zuwa, ni Ubangiji Allah na faɗa.

9. Sa'an nan su mazaunan biranen Isra'ila za su tattara makaman mutane, wato garkuwoyi, da bakuna, da kibau da kulake, da māsu, su yi ta hura wuta da su, har ya kai shekara bakwai.

10. Ba za su yi wahalar zuwa jeji don nemo itacen wuta ba, gama za su yi ta hura wuta da makaman. Za su washe waɗanda suka washe su a dā, ni Ubangiji na faɗa.

11. “A wannan rana zan ba Gog makabarta a Isra'ila, a kwarin matafiya a gabashin teku. Makabartar za ta kashe hanyar matafiya, gama a can za a binne Gog da dukan rundunar da take tare da shi. Za a kira wurin Hamongog, wato Kwarin Rundunar Gog.

12. Jama'ar Isra'ila za su yi wata bakwai suna binne su don su tsabtace ƙasar.

13. Dukan jama'ar ƙasar za su yi aikin binnewar, zai zama daraja a gare su a ranar da zan bayyana ɗaukakata, ni Ubangiji Allah na faɗa.

14. A ƙarshen wata bakwai ɗin za su keɓe waɗansu mutane domin su bi ko'ina cikin ƙasar, su binne sauran gawawwakin da suka ragu a ƙasar don su tsabtace ta.

15. Sa'ad da waɗannan suke bibiyawa a cikin ƙasar, duk wanda ya ga ƙashin mutum, sai ya kafa wata alama kusa da ƙashin don masu binnewa su gani, su ɗauka, su binne a Kwarin Rundunar Gog.

Karanta cikakken babi Ez 39