Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 34:1-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,

2. “Ɗan mutum, ka yi annabci a kan makiyayan Isra'ila, ka ce musu, ‘Ku masu kiwon mutanen Isra'ila, ni Ubangiji Allah na ce, kaito, kaito, ku masu kiwon mutanen Isra'ila, kuna kiwon kanku kawai! Ashe, ba makiyaya ne suke kiwon tumaki ba?

3. Kuna cin kitsensu, kuna yi wa kanku tufafi da gashinsu, kukan yanka turkakkun, amma ba ku yi kiwon tumakin ba.

4. Ba ku ƙarfafa marasa ƙarfi ba, ba ku warkar da marasa lafiya ba, ba ku ɗora karayyu ba, waɗanda kuma suka yi makuwa ba ku komar da su ba, waɗanda suka ɓace ba ku nemo su ba, amma kuka mallake su ƙarfi da yaji.

5. Sai suka warwatsu saboda rashin makiyayin kirki, suka zama abincin namomin jeji.

6. Tumakina sun watse, suna yawo a kan dukan duwatsu da tuddai, sun warwatsu a duniya duka, ba wanda zai nemo su.’

7. “Domin haka, ku ji maganata, ku makiyaya.

8. Ni Ubangiji Allah na ce, ‘Hakika da yake tumakina sun zama ganimar dukan namomin jeji, saboda rashin makiyayin kirki, makiyayana kuma ba su nemo su ba, amma suka yi kiwon kansu, ba su yi kiwon tumakin ba,

9. to, ku makiyaya, sai ku saurara ga maganata.

10. Ga shi, ina gāba da ku, zan nemi tumakina a hannunku. Zan hana ku yin kiwon tumakin, ku kuma ba za ku ƙara yin kiwon kanku ba. Zan ƙwace tumakina daga hannunku, domin kada su ƙara zama abincinku.”’

11. “Ni Ubangiji Allah na ce, ni kaina zan nemi tumakina.

12. Kamar yadda makiyayi yakan nemo tumakin da suka watse daga cikin garkensa, haka zan nemi tumakina. Zan cece su daga dukan wuraren da aka watsar da su a ranar gizagizai da baƙin duhu.

13. Zan fito da su daga cikin sauran al'umma, in tattaro su daga ƙasashe dabam dabam, in kawo su ƙasarsu, in yi kiwonsu a kan tuddan Isra'ila, kusa da maɓuɓɓugai, da cikin dukan wuraren da mutane suke zaune a ƙasar.

Karanta cikakken babi Ez 34