Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 33:10-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. “Kai ɗan mutum, sai ka faɗa wa mutanen Isra'ila, ‘Kuna cewa, “Laifofinmu da zunubanmu suna nawaita mana, muna kuwa lalacewa, yanzu fa, ta ƙaƙa za mu rayu?” ’

11. Ka faɗa musu, ni Ubangiji Allah, na ce, ‘Hakika, ba na murna da mutuwar mugu, amma na fi so mugun ya bar hanyarsa ya rayu. Ku juyo, ku juyo daga mugayen hanyoyinku, gama don me za ku mutu, ya mutanen Isra'ila?’

12. “Ɗan mutum, sai kuma ka faɗa wa mutanenka, cewa adalcin adali ba zai cece shi ba sa'ad da ya yi laifi, muguntar mugu kuma ba za ta sa ya mutu ba idan ya bar muguntarsa. Adalcin adali ba zai cece shi ba, idan ya shiga aikata zunubi.

13. Idan na ce wa adali, ba shakka zai rayu, amma idan ya dogara ga adalcin da ya riga ya yi, sa'an nan ya shiga aikata laifi, ba za a tuna da ayyukan adalcinsa na dā ba. Zai mutu saboda laifin da ya yi.

14. Idan kuma na ce wa mugu ba shakka zai mutu, amma idan ya bar laifinsa, ya shiga aikata adalci,

15. idan kuma ya mayar da jingina, ya mayar da abin da ya ƙwace, sa'an nan ya kiyaye dokokin rai, ya daina yin laifi, hakika, zai rayu, ba zai mutu ba.

16. Ba za a tuna da laifofin da ya aikata a dā ba, gama ya aikata adalci da gaskiya, zai rayu.

17. “Amma mutanenka sun ce, ‘Hanyar Ubangiji ba daidai ba ce,’ alhali kuwa tasu ce ba daidai ba.

18. Sa'ad da adali ya daina aikata adalci, ya shiga aikata laifi, zai mutu saboda laifinsa.

19. Sa'ad da kuma mugu ya daina aikata mugunta, ya shiga aikata adalci da gaskiya, zai rayu saboda adalcinsa.

20. Amma duk da haka kun ce, ‘Hanyar Ubangiji ba daidai ba ce.’ Ya mutanen Isra'ila, zan hukunta kowane ɗayanku gwargwadon ayyukansa.”

21. A rana ta biyar ga watan goma, a shekara ta goma sha biyu ta zaman bautar talala da aka kai mu, sai wani ɗan gudun hijira daga Urushalima ya zo wurina, ya ce, “Birnin ya fāɗi.”

22. A maraicen da ya wuce kafin ɗan gudun hijirar ya iso, Ubangiji ya ƙarfafa ni, ya kuma buɗe bakina a lokacin da mutum ya zo wurina da safe. Bakina kuwa ya buɗe, ban zama bebe ba kuma.

23. Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,

24. “Ɗan mutum, mazaunan wuraren nan da aka lalatar a ƙasar Isra'ila, suna cewa, ‘Ibrahim shi kaɗai ne, duk da haka an ba shi ƙasar duka, balle fa mu da muke da yawa, lalle ƙasar tamu ce.’

25. “Domin haka, sai ka faɗa musu, ‘Ubangiji Allah ya ce, “Kuna cin nama da jininsa, kuna bautar gumaka, kuna kuma yin kisankai, da haka za ku mallaki ƙasar?

Karanta cikakken babi Ez 33