Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 31:12-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Baƙi mafi bantsoro daga cikin al'ummai sun sare shi, sun bar shi. Rassansa sun faɗi a kan duwatsun da suke cikin dukan kwaruruka, rassansa kuma sun kakkarye, sun faɗi a cikin dukan magudanan ruwa na ƙasa. Dukan mutanen duniya sun tashi daga inuwarsa, sun bar shi.

13. Dukan tsuntsayen sararin sama za su zauna a gorarsa. Namomin jeji kuma za su yi ta yawo a cikin rassansa.

14. An yi wannan domin kada itatuwan da suke bakin ruwa su yi girma, su yi tsayi da yawa har kawunansu su kai cikin gizagizai, domin kuma kada itacen da yake shan ruwa ya yi tsayi kamarsa, gama an bashe su ga mutuwa zuwa lahira, tare da 'yan adam masu gangarawa zuwa cikin kabari.”

15. Ubangiji Allah ya ce, “A ranar da ya gangara zuwa lahira, na sa zurfi ya rufe shi, ya yi makoki dominsa. Na tsai da kogunansa, yawan ruwansa ya ƙafe. Na sa Lebanon ta yi duhu saboda shi. Dukan itatuwan jeji kuwa sun yi yaushi saboda shi.

16. Al'ummai suka yi rawar jiki saboda amon faɗuwarsa, sa'ad da na jefar da shi cikin lahira tare da waɗanda suke gangarawa zuwa cikin kabari. Dukan itatuwan Aidan da itatuwa mafi kyau na Lebanon waɗanda suka ƙoshi da ruwa, sun ta'azantu a lahira.

17. Su kuma suka gangara tare da shi zuwa lahira, suka tarar da waɗanda aka kashe da takobi, wato waɗanda daga cikin al'ummai suka yi zama a inuwarsa.

18. “A cikin itatuwan Aidan, da wa za a kamanta darajarka da girmanka? Duk da haka za a kai ka lahira tare da itatuwan Aidan. Za ka zauna tare da marasa kaciya, da waɗanda aka kashe da takobi. Wannan Fir'auna ke nan, da dukan jama'arsa, ni Ubangiji Allah na faɗa.”

Karanta cikakken babi Ez 31