Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 27:22-34 Littafi Mai Tsarki (HAU)

22. 'Yan kasuwar Sheba da Ra'ama sun sayi kayanki da kayan yaji mafi kyau iri iri, da duwatsu masu daraja iri iri, da zinariya.

23. Garuruwan Haran, da Kanne, da Aidan, da fataken Sheba, da Asshur, da Kilmad sun yi ciniki da ke.

24. Sun sayar miki da tufafi masu tsada, da na shuɗi, da masu ado, da darduma masu ƙyalƙyali da kirtani, da igiyoyi waɗanda aka tufka da kyau.

25. Jiragen ruwan Tarshish suna jigilar kayan cinikinki.Don haka kin bunƙasa,Kin ɗaukaka a tsakiyar tekuna.

26. “ ‘Matuƙanki sun kai ki cikin babbar teku,Iskar gabas ta farfasa ki a tsakiyar teku.

27. Dukiyarki, da kayan cinikinki, da hajarki,Da ma'aikatanki da masu ja miki gora,Da masu tattoshe mahaɗan katakanki,Da abokan cinikinki, da dukan sojojinki,Da dukan taron jama'ar da take tare da ke,Sun dulmuya cikin tsakiyar teku a ranar halakarki.

28. Saboda kukan masu ja miki gora, ƙasa ta girgiza.

29. “ ‘Daga cikin jiragen ruwansu dukan waɗanda suke riƙe da matuƙi za su zo.Matuƙan jiragen ruwa da masu jagora za su tsaya a gaɓar teku.

30. Za su yi kuka mai zafi dominki.Za su yi hurwa, su yi birgima cikin toka.

31. Za su aske kansu saboda ke, su sa tufafin makoki.Za su yi kuka mai zafi dominki.

32. A cikin makokinsu dominki, suna kuka, suna cewa,Wa yake kama da Taya,Ita wadda take shiru a tsakiyar teku?

33. Sa'ad da kayan cinikinki suka tafi ƙasashen hayi,Kin wadatar da al'ummai,Kin arzuta sarakunan duniya da yawan dukiyarki da hajarki.

34. Yanzu teku ta farfashe ki cikin zurfafa,Hajarki da dukan ma'aikatan jirgin ruwanki sun nutse tare da ke.

Karanta cikakken babi Ez 27