Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 26:3-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. domin haka ni, Ubangiji Allah na ce, ‘Ina gāba da ke, ke Taya, zan kawo al'ummai da yawa su yi gāba da ke, kamar yadda teku takan kawo raƙuman ruwa.

4. Za su hallaka garun Taya, su rurrushe hasumiyarta. Zan ƙan'kare ƙasarta, in maishe ta fā.

5. Za ta zama wurin shanya taruna a tsakiyar teku. Za ta kuma zama ganima ga sauran al'umma. Ni Ubangiji na faɗa.

6. Ya'yanta mata waɗanda suke zaune a filin kasar za a kashe su da takobi, sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji.’ ”

7. Gama Ubangiji Allah ya ce, “Zan kawo wa Taya Nebukadnezzar, Sarkin Babila, sarkin sarakuna, daga arewa. Zai zo da dawakai da karusai, da sojojin dawakai, da babbar rundunar sojoji.

8. Zai kashe ya'yanki mata waɗanda suke a filin ƙasar da takobi. Zai kuma kewaye ki da garun yaƙi, ya gina miki mahaurai, sa'an nan zai rufe ki da garkuwoyi.

9. Zai rushe garunki da dundurusai, ya rushe hasumiyarki da gatura.

10. Saboda yawan dawakansa, ƙurar da za su tayar za ta rufe ki. Garunki kuma zai girgiza saboda motsin sojojin doki, da na ƙafafu kamar na keke, da na karusai sa'ad da ya shiga ƙofofinki, kamar yadda akan shiga birnin da garunsa ya rushe.

11. Kofatan dawakansa za su tattake dukan titunanki, zai kashe mutanenki da takobi. Manyan ginshiƙanki za su rushe.

12. Za su washe dukiyarki da kayan cinikinki. Za su kuma rurrushe garunki da kyawawan gidajenki. Za su kwashe duwatsu, da katakai, da tarkace, su zubar a cikin teku.

13. Zan sa a daina raira waƙoƙi da kaɗa garayu.

14. Zan maishe ki fā, wato wurin shanya taruna. Ba za a sāke gina ki ba, ni Ubangiji Allah na faɗa.”

Karanta cikakken babi Ez 26