Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 24:14-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Ni, Ubangiji na faɗa, zai tabbata gama zan aikata, ba zan fasa ba, ba kuwa zan ƙyale ba, ba kuma zan bari ba. Zan hukunta ki saboda hanyoyinki da ayyukanki, ni Ubangiji Allah na faɗa ”

15. Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,

16. “Ya ɗan mutum, ga shi, ina gab da ɗauke maka ƙaunatacciyarka farat ɗaya, amma fa, kada ka yi makoki, ko kuka, ko ka zubar da hawaye.

17. Ka yi ajiyar zuciya a hankali, kada ka yi makoki saboda matacciyar. Ka naɗa rawaninka, ka sa takalmanka, kada ka ja amawali, kada kuma ka ci abincin masu makoki.”

18. Sai na yi magana da mutane da safe, da maraice kuwa matata ta rasu. Kashegari da safe, sai na yi kamar yadda aka umarce ni.

19. Mutane kuwa suka tambaye ni dalilin da ya sa nake yin haka.

20. Sai na ce musu, “Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,

21. in faɗa wa mutanen Isra'ila, cewa Ubangiji Allah ya ce, ‘Zan ƙazantar da Haikalina, abin fariyarku, da abin da idanunku suke jin daɗin ganinsa, da abin faranta zuciyarku. 'Ya'yanku maza waɗanda kuka bari a baya, za a kashe su da takobi.

Karanta cikakken babi Ez 24