Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 20:15-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Na kuma rantse musu a cikin jeji, cewa ba zan kai su ƙasar da na ba su ba, ƙasar da take cike da yalwar albarka, wato ƙasar da take mafi albarka duka,

16. domin sun ƙi su bi ka'idodina da dokokina. Suka ɓata ranar Asabar ɗina, gama zuciyarsu ta fi so ta bauta wa gumaka.

17. “Duk da haka na yafe musu, ban hallaka su ba, ban kuma shafe su a jeji ba.

18. Sai na ce wa 'ya'yansu a jeji, ‘Kada ku bi dokokin ubanninku, ko kuwa ku kiyaye ka'idodinsu, kada kuma ku ɓata kanku da gumakansu.

19. Ni ne Ubangiji Allahnku, ku kiyaye dokokina da ka'idodina sosai.

20. Ku kiyaye ranar Asabar ɗina domin ta zama alama tsakanina da ku, domin kuma ku sani ni ne Ubangiji Allahnku.’

21. “Amma 'ya'yansu suka tayar mini, ba su kiyaye dokokina da ka'idodina ba, waɗanda idan mutum ya kiyaye su, zai rayu. Suka kuma ɓata ranar Asabar ɗina. Sai na yi tunani zan zubo musu da hasalata, in aukar da fushina a kansu a jeji.

22. Amma na yi haƙuri saboda sunana, domin kada a saɓi sunana a gaban sauran al'umma waɗanda suka gani na fito da mutanen Isra'ila daga ƙasar Masar.

23. Na rantse musu a jeji, cewa zan warwatsar da su cikin sauran al'umma, da sauran ƙasashe

24. domin ba su kiyaye ka'idodina da dokokina ba, suka ɓata ranar Asabar ɗina, suka bauta wa gumakan kakanninsu.

25. Sai kuma na ba su dokoki da ƙa'idodi marasa amfani, waɗanda ba za su rayu ta wurinsu ba.

26. Na kuma bari su ƙazantar da kansu ta wurin hadayunsu, su kuma sa 'ya'yan farinsu su ratsa wuta. Na yi haka don in sa su zama abin ƙyama, don kuma su sani ni ne Ubangiji.

27. “Domin haka, ya ɗan mutum, ka yi magana da mutanen Isra'ila ka ce, ‘Ni Ubangiji Allah, na ce kakanninku sun saɓe ni da ba su amince da ni ba.

28. Gama sa'ad da na kawo su cikin ƙasar da na rantse zan ba su, sa'ad da suka ga kowane tudu da kowane itace mai ganye, sai suka miƙa hadayunsu a wuraren nan suka tsokane ni da hadayunsu. A wuraren ne suka miƙa hadayunsu na turare mai ƙanshi da hadayu na sha.’

Karanta cikakken babi Ez 20