Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 17:12-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. “Ka tambayi mutanen Isra'ila, 'yan tawayen nan cewa, ‘Ba ku san ma'anar waɗannan abubuwa ba?’ Ka faɗa musu, cewa Sarkin Babila ya zo Urushalima, ya tafi da sarkinta da shugabanninta zuwa Babila.

13. Sai ya dauƙi wani daga zuriyar sarauta, ya yi alkawari da shi, ya kuma rantsar da shi. Ya kwashe mutanen ƙasa masu maƙami,

14. don sarautar ƙasar ta raunana, ta kāsa ɗaga kanta, amma ta tsaya dai ta wurin cika alkawarinsa.

15. Amma Sarkin Yahuza ya tayar masa, da ya aiki wakilai zuwa Masar don a ba shi dawakai da sojoji masu yawa. To, zai yi nasara? Wanda ya yi irin wannan abu zai tsira? Zai iya ta da alkawari sa'an nan ya tsere?

16. “Ni Ubangiji Allah, na ce, hakika wannan sarki zai mutu a Babila, domin bai cika rantsuwarsa da alkawarin da ya yi wa Sarkin Babila, wanda ya naɗa shi ba.

17. Fir'auna da yawan sojojinsa masu ƙarfi, ba za su taimake shi da yaƙin ba, sa'ad da Babilawa suka gina mahaurai da kagarai don su kashe mutane da yawa.

18. Bai kuwa cika rantsuwarsa da alkawarinsa ba. Ya ƙulla alkawari, amma ga shi, ya aikata dukan waɗannan abubuwa, ba zai kuɓuta ba.

19. “Domin haka ni Ubangiji Allah, na ce, hakika zan nemi hakkin rantsuwar da ya yi mini, da alkawarin da ya yi mini, waɗanda bai cika ba.

20. Zan kafa masa tarko in kama shi, sa'an nan in kai shi Babila inda zan yi masa shari'a saboda ya tayar mini.

21. Dukan sojojinsa zaɓaɓɓu za a kashe su da takobi, za a watsar da waɗanda suka ragu ko'ina. Za ku sani ni Ubangiji ne na faɗa.”

22. Ga abin da Ubangiji Allah ya ce,“Ni kaina zan cire toho a kan itacen al'ul mai tsawo.Daga cikin sababbin rassansa zan karya lingaɓu,In dasa shi a tsauni mai tsayi.

23. A ƙwanƙolin tsaunin Isra'ila zan dasa shiDon ya fito da rassa, ya ba da 'ya'ya,Ya zama itacen al'ul na gaske.Tsuntsaye iri iri za su zauna a ƙarƙashinsa,Za su yi sheƙuna a cikin inuwar rassansa.

24. Dukan itatuwan jeji za su sani,Ni Ubangiji nakan sa manyan itatuwa su zama ƙanana,In sa ƙanana kuma su zama manya,In sa ɗanyen itace ya bushe,In sa busasshen itace kuma ya zama ɗanye, Ni Ubangiji na faɗa, zan kuwa aikata.”

Karanta cikakken babi Ez 17