Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 11:1-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sai Ruhu ya ɗaga ni sama, ya kai ni ƙofar gabas ta Haikalin Ubangiji wadda dake fuskantar gabas. Sai ga mutum ashirin da biyar a bakin ƙofar. A cikinsu na ga Yazaniya ɗan Azzur, da Felatiya ɗan Benaiya, shugabannin jama'a.

2. Sai ya ce mini, “Ɗan mutum, waɗannan su ne mutanen da suke ƙulla mugunta, waɗanda suke ba da muguwar shawara a cikin birnin.

3. Waɗanda suke cewa, ‘Lokacin gina gidaje bai yi kusa ba. Wannan birni tukunya ce mai ɓararraka, mu ne kuwa naman.’

4. Saboda haka ka yi musu annabci marar kyau, ka yi annabci, ya ɗan mutum!”

5. Sa'an nan Ruhun Ubangiji ya sauko a kaina, ya ce mini, “Ka ce, ‘In ji Ubangiji, haka kuke tunani, ku mutanen Isra'ila, gama na san abin da yake cikin zuciyarku.

6. Kun kashe mutane da yawa a wannan birni, har kun cika titunansa da gawawwaki.’

7. “Domin haka Ubangiji Allah ya ce, ‘Gawawwakin da kuka shimfiɗa a cikin birnin su ne naman, birnin kuwa shi ne tukunya mai ɓararraka, amma za a fitar da ku daga cikinsa.

8. Kun tsorata saboda takobi, ni kuwa zan kawo muku takobi,’ in ji Ubangiji Allah.

9. ‘Zan fitar da ku daga cikin birnin, in bashe ku a hannun baƙi, zan hukunta ku.

10. Za a kashe ku da takobi. Zan hukunta ku duk inda kuke a Isra'ila, sa'an nan za ku sani ni ne Ubangiji.

11. Birnin ba zai zama muku tukunya mai ɓararraka ba, ba kuwa za ku zama nama a cikinsa ba. Zan hukunta ku duk inda kuke a Isra'ila.

12. Za ku kuwa sani ni ne Ubangiji, gama ba ku kiyaye dokokina da ka'idodina ba, amma kuka kiyaye ka'idodin sauran al'umma waɗanda suke kewaye da ku.”’

13. Sa'ad da nake yin annabci, sai Felatiya ɗan Benaiya, ya rasu. Sai na faɗi rubda ciki na fashe da kuka, na ce, “Ya Ubangiji Allah, za ka ƙare sauran mutanen Isra'ila ƙaƙaf ne?”

14. Ubangiji kuwa ya yi magana da ni, ya ce,

Karanta cikakken babi Ez 11