Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 10:4-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Ɗaukakar Ubangiji ta tashi daga kan kerubobin zuwa ƙofar Haikalin. Girgije kuwa ya cika Haikalin, hasken zatin Ubangiji ya cika farfajiyar.

5. Sai aka ji amon fikafikan kerubobin a filin da yake can waje, kamar muryar Allah Maɗaukaki sa'ad da yake magana.

6. Ya kuwa umarci wanda yake saye da lilin ɗin, ya ce, “Ka ɗibi wuta daga ƙarƙashin ƙafafun da suke tsakanin kerubobin.” Sai ya tafi ya tsaya a gefen ƙafar.

7. Kerub kuwa ya miƙa hannunsa daga tsakanin kerubobi zuwa wurin wutar da take tsakanin kerubobin, ya ɗebo wutar, ya zuba a ahannun mutumin da yake saye da rigar lilin. Shi kuwa ya karɓa, ya fita.

8. Kerubobin suna da hannuwa kamar na 'yan adam a ƙarƙashin fikafikansu.

9. Da na duba, sai na ga ƙafa guda huɗu kusa da kerubobin. Kowane kerub yana da ƙafa ɗaya kusa da shi. Ƙafafun suna ƙyalli kamar wani dutse mai daraja.

10. Dukansu kuwa kamanninsu ɗaya, kamar ƙafa a cikin ƙafa.

11. Sa'ad da suke tafiya, sukan tafi kowane waje, ba sai sun juya ba. Duk wajen da ƙafar gaba ta nufa, nan sauran za su bi, ba sai sun juya ba.

12. Suna da idanu a jikunansu ko'ina, a bayansu, da hannuwansu, da fikafikansu da kuma ƙafafunsu.

13. Na ji ana kiran ƙafafun, ƙafafun guguwa.

14. Kowane kerub yana da fuska huɗu. Fuska ta fari ta kerub ce, fuska ta biyu ta mutum ce, fuska ta uku ta zaki ce, fuska ta huɗu kuwa ta gaggafa ce.

15. Kerubobin kuwa suka tashi sama. Waɗannan su ne talikai huɗu waɗanda na gani a bakin kogin Kebar.

16. Sa'ad da kerubobin suka tafi, ƙafafun kuma sukan tafi tare da su. Sa'ad da suka ɗaga fikafikansu don su tashi daga ƙasa zuwa sama, ƙafafun kuma ba su barinsu.

17. Sa'ad da suka tsaya cik, sai ƙafafun su ma su tsaya cik, sa'ad da suka tashi sama, sai su kuma su tashi tare da su, gama ruhun talikan yana cikinsu.

Karanta cikakken babi Ez 10