Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 1:13-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. A tsakiyar talikan akwai wani abu mai kama da garwashin wuta, kamar jiniyoyi kuma suna kai da kawowa a tsakanin talikan, wutar kuwa tana haskakawa. Daga cikin wutar kuma, sai ga walƙiya tana fitowa.

14. Talikan kuma suka yi ta giftawa suna kai da kawowa kamar walƙiya.

15. Da na dubi talikan, sai na ga ƙafafu huɗu kamar na keke a ƙasa kusa da talikan. Ɗaya domin kowane taliki.

16. Ga kamannin ƙafafun da yadda aka yi su. Suna ƙyalƙyali kamar duwatsu masu daraja. Dukansu huɗu fasalinsu ɗaya ne. An yi su kamar wata ƙafa tana cikin wata ƙafa.

17. Sa'ad da suke tafiya, suna tafiya a kowane waje, ba sai sun juya ba.

18. Akwai waɗansu ƙarafa kamar zobe, da idanu kuma tantsai kewaye da ƙafafun.

19. Duk sa'ad da talikan suka motsa, sai kuma ƙafafun su motsa tare da su. Idan kuma talikan suka ɗaga sama, sai ƙafafun su ɗaga tare da su.

20. Duk inda ruhu ya nufa, sai talikan su bi, sai kuma ƙafafun su tafi tare da su, gama ruhun talikan yana cikin ƙafafun.

21. Idan talikan sun motsa, sai ƙafafun kuma su motsa. Idan sun tsaya cik, sai su ma su tsaya. Idan kuma talikan sun ɗaga sama, sai ƙafafun su ɗaga sama tare da su, gama ruhun talikan yana cikin ƙafafun.

22. Sama da talikan akwai kamannin al'arshi mai walƙiya kamar madubi.

23. A ƙarƙashin al'arshin fikafikansu sun miƙe kyam daura da juna. Kowane taliki yana da fikafikai biyu da su yake rufe jikinsa.

24. Sa'ad da suke tafiya, sai na ji motsin fikafikansu kamar amon ruwa, kamar kuma muryar tsawar Maɗaukaki, kamar hayaniyar runduna. Idan sun tsaya cik, sai su saukar da fikafikansu.

25. Sai aka ji murya ta fito daga saman al'arshi ɗin.

26. A saman al'arshin akwai wani abu mai kamar kursiyin sarauta da aka yi da yakutu. Akwai wani kamar mutum yana zaune a kan abin nan mai kama da kursiyin sarauta.

27. Daga kwankwasonsa zuwa sama yana walƙiya kamar tagullar da aka kewaye ta da wuta. Daga kwankwasonsa zuwa ƙasa yana haskakawa kamar wuta.

Karanta cikakken babi Ez 1