Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Esta 6:10-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Sai sarki ya ce wa Haman, “Yi maza, ka ɗauki rigunan da dokin, ka tafi wurin Mordekai, Bayahuden nan, wanda yakan zauna a ƙofar sarki ka yi masa kamar yadda ka faɗa. Kada ka kasa yin kome daga cikin abin da ka faɗa.”

11. Haman kuwa ya ɗauki rigunan da dokin. Ya sa wa Mordekai riguna, ya hawar da shi kan dokin, ya zagaya da shi a dandalin birnin, yana cewa, “Haka za a yi wa wanda sarki yake so ya ɗaukaka.”

12. Sa'an nan Mordekai ya koma ƙofar sarki, Haman kuwa ya gaggauta zuwa gidansa, yana baƙin ciki, kunya ta rufe shi.

13. Da ya koma gida, sai ya faɗa wa Zeresh, matarsa, da dukan abokansa, duk abin da ya same shi. Sai mutanensa masu hikima da Zeresh, matarsa, suka ce masa, “Idan Mordekai, wanda ka fara faɗuwa a gabansa, in dai daga zuriyar Yahudawa yake, to, ba za ka yi nasara a kansa ba, amma hakika za ka fāɗi a gabansa.”

Karanta cikakken babi Esta 6