Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Dan 8:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A shekara ta uku ta sarautar Belshazzar, sai ni Daniyel na ga wahayi bayan wancan na fari.

2. A wahayin sai na gani ina a bakin kogin Ulai a Shushan, masarautar lardin Elam.

3. Da na ta da idanuna, sai na ga rago a tsaye a gāɓar kogin. Yana da ƙaho biyu dogaye, amma ɗaya ya ɗara ɗaya tsawo. Wanda ya ɗara tsawon shi ne ya tsiro daga baya.

4. Na ga ragon ya kai karo wajen yamma da wajen kudu, da wajen arewa. Ba wata dabbar da ta iya karawa da shi, ba wanda kuma zai iya kuɓuta daga ikonsa, ya yi yadda ya ga dama, ya ɗaukaka kansa.

5. Sa'ad da nake cikin tunani, sai ga bunsuru ya ɓullo daga wajen yamma, ya ratsa dukan duniya, ba ya ko taɓa ƙasa. Akwai ƙaho na gaske a tsakanin idanunsa.

6. Sai ya zo wurin ragon, mai ƙahoni biyu, wanda na gani a tsaye a gāɓar kogi. Bunsurun kuwa ya tasar masa da fushi mai zafi.

7. Na ga ya zo kusa da ragon, ya husata da shi ƙwarai, sai ya gabza wa ragon karo. Ya kakkarya ƙahonin nan nasa biyu. Ƙarfin ragon ya kāsa, ba ya iya kare kansa daga bunsurun. Bunsurun ya buge shi ƙasa ya tattake shi. Ba wanda ya iya ceton ragon daga bunsurun.

8. Sa'an nan bunsurun ya ɗaukaka kansa ƙwarai, amma sa'ad da ya ƙasaita sai babban ƙahon nan ya karye, a maimakonsa sai waɗansu ƙahoni huɗu na gaske suka tsiro suna fuskantar kusurwa huɗu.

9. Wani ƙaramin ƙaho kuma ya tsiro daga cikin ɗayansu, ya yi girma ya ƙasaita ƙwarai. Ya nuna ikonsa wajen gabas, da wajen kudu, da wajen ƙasa mai albarka.

10. Ya ƙasaita, har ya kai cikin rundunar sama. Ya jawo waɗansu taurari zuwa ƙasa, ya tattake su.

11. Ya ɗaukaka kansa, har ya mai da kansa daidai da shugaban runduna. Ya hana yin hadayar ƙonawa ta yau da kullum ga Sarkin sarakuna, ya kuma rushe masa wuri mai tsarki.

12. Saboda zunubi sai aka ba da runduna duk da hadayar ƙonawa ta yau da kullum ga ƙahon. Sai ya yi watsi da gaskiya, ya yi abin da ya ga dama, ya kuwa yi nasara.

Karanta cikakken babi Dan 8