Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Dan 2:36-44 Littafi Mai Tsarki (HAU)

36. “Wannan shi ne mafarkin, yanzu kuma za mu faɗa wa sarki fassararsa.

37. Ya sarki, kai ne sarkin sarakuna wanda Allah na Sama ya ba ka sarauta, da iko, da ƙarfi, da daraja.

38. A hannunka kuma ya ba da dukan wurare inda 'yan adam, da dabbobi, da tsuntsaye suke zama. Ya sa ka ka mallake su duka. Kai ne kan zinariyan nan na mutum-mutumin.

39. A bayanka kuma za a yi wani mulki wanda bai kai kamar naka ba. Za a yi wani mulki kuma na uku mai darajar tagulla, wanda zai mallaki dukan duniya.

40. Za a kuma yi mulki na huɗu, mai ƙarfi kamar baƙin ƙarfe. Da yake baƙin ƙarfe yakan kakkarya, ya ragargaje abubuwa, haka nan wannan mulki zai ragargaje sauran mulkoki.

41. Ka kuma ga an yi ƙafafun da yatsotsin da baƙin ƙarfe gauraye da yumɓu, wato mulkin zai rabu, amma zai kasance da ƙarfi kamar na baƙin karfen da yake gauraye da yumɓu.

42. Kamar yadda yatsotsin ƙafafun rabi baƙin ƙarfe, rabi kuma yumɓu ne, haka nan mulkin zai kasance, rabi da ƙarfi, rabi kuma da gautsi.

43. Kamar yadda ka ga baƙin ƙarfen ya gauraya da yumɓun, haka nan mulkokin za su gauraye da juna ta wurin aurayya, amma ba za su haɗu da juna ba, kamar yadda baƙin ƙarfe da yumɓu ba su haɗuwa.

44. A kwanakin waɗannan sarakuna, Allah na Sama zai kafa wani mulki wanda ba zai taɓa rushewa ba har abada, ba kuma za a gādar da shi ga waɗansu mutane ba. Wannan mulki zai ragargaje dukan waɗannan mulkoki, ya kawo ƙarshensu. Wannan mulki zai dawwama har abada.

Karanta cikakken babi Dan 2