Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 9:8-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allahnka wanda yake murna da kai, wanda ya hawar da kai gadon sarautarsa, don ka zama sarki a gaban Ubangiji Allahnka. Gama Allah yana ƙaunar Isra'ila, zai kuwa tabbatar da su har abada, shi ya sa ya naɗa ka sarkinsu, don ka aikata gaskiya da adalci.”

9. Sa'an nan kuma ta ba sarki zinariya talanti ɗari da ashirin, da kayan yaji masu yawan gaske, da duwatsu masu daraja. Irin kayan yajin da Sarauniyar Sheba ta ba sarki Sulemanu ba irinsa.

10. Bayan haka kuma barorin Hiram tare da barorin Sulemanu waɗanda suka kawo zinariya daga Ofir, sun kuma kawo itatuwan algum da duwatsu masu daraja.

11. Da itatuwan algum ɗin, sarki ya yi matakan Haikalin Ubangiji da na fādar sarki, ya kuma yi garayu, da molaye saboda mawaƙa. Ba a taɓa ganin irinsu a ƙasar Yahuza ba.

12. Sarki Sulemanu kuwa ya ba Sarauniyar Sheba duk abin da ranta take bukata, da iyakar abin da take so, banda abin da ta kawo wa sarki. Sa'an nan ta koma ƙasarta, ita da barorinta.

13. Yawan zinariya da Sulemanu yake samu a shekara guda, talanti ɗari shida da sittin da shida,

14. banda wadda 'yan kasuwa da fatake sukan kawo masa. Dukan sarakunan Arabiya da masu mulkin ƙasar kuma sun kawo wa Sulemanu zinariya da azurfa.

15. Sai Sulemanu sarki ya ƙera manyan garkuwoyi guda ɗari biyu na zinariya, kowace garkuwa nauyinta shekel ɗari shida ne na zinariya.

16. Ya kuma ƙera garkuwa ɗari uku ƙanana na zinariya, kowace garkuwa nauyinta shekel ɗari uku ne. Sarki fa ya ajiye su a gidan da aka gina da katakai daga Lebanon.

17. Sarki ya yi babban gadon sarauta na hauren giwa, ya dalaye shi da zinariya.

18. Gadon sarautar yana da matakai da 'yar kujerar zinariya ta ɗora ƙafa haɗe da gadon. A kowane gefen gadon an yi wurin ɗora hannu, akwai kuma siffar zaki a tsaye kusa da kowane wurin ɗora hannun.

Karanta cikakken babi 2 Tar 9