Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 9:3-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Sa'ad da Sarauniyar Sheba ta ga hikimar Sulemanu, da gidan da ya gina,

4. da irin abincin da yake kan tebur ɗinsa da irin zaman manyan mutanensa, da barorin da yake yi masa hidima, da irin tufafinsu, da masu ba da abin sha, da irin tufafinsu, ta kuma ga hadayun ƙonawa da yake miƙawa a Haikalin Ubangiji, sai ta ji ba ta da sauran kuzari.

5. Sarauniya ta ce wa sarkin, “Ashe, gaskiya ce, labarinka da na ji a ƙasata a kan al'amuranka da hikimarka.

6. Amma dā ban gaskata labarinsu ba, sai da na zo na gani da idona, ashe, ko rabin yawan hikimarka ma ba a faɗa mini ba. Ashe, duk labarin da aka faɗa mini, ka zarce haka ƙwarai.

7. Masu farin ciki ne mutanenka, da barorinka waɗanda suke yi maka hidima kullayaumin, gama kullum suna jin hikimarka.

8. Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allahnka wanda yake murna da kai, wanda ya hawar da kai gadon sarautarsa, don ka zama sarki a gaban Ubangiji Allahnka. Gama Allah yana ƙaunar Isra'ila, zai kuwa tabbatar da su har abada, shi ya sa ya naɗa ka sarkinsu, don ka aikata gaskiya da adalci.”

9. Sa'an nan kuma ta ba sarki zinariya talanti ɗari da ashirin, da kayan yaji masu yawan gaske, da duwatsu masu daraja. Irin kayan yajin da Sarauniyar Sheba ta ba sarki Sulemanu ba irinsa.

10. Bayan haka kuma barorin Hiram tare da barorin Sulemanu waɗanda suka kawo zinariya daga Ofir, sun kuma kawo itatuwan algum da duwatsu masu daraja.

11. Da itatuwan algum ɗin, sarki ya yi matakan Haikalin Ubangiji da na fādar sarki, ya kuma yi garayu, da molaye saboda mawaƙa. Ba a taɓa ganin irinsu a ƙasar Yahuza ba.

12. Sarki Sulemanu kuwa ya ba Sarauniyar Sheba duk abin da ranta take bukata, da iyakar abin da take so, banda abin da ta kawo wa sarki. Sa'an nan ta koma ƙasarta, ita da barorinta.

Karanta cikakken babi 2 Tar 9