Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 9:21-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Sau ɗaya a shekaru uku, sarki yakan aika da jiragen ruwa zuwa Tarshish tare da barorin Hiram, su kawo zinariya, da azurfa, da hauren giwa, da manyan birai, da ɗawisu.

22. Sarki Sulemanu ya fi dukan sarakunan duniya dukiya da hikima.

23. Sarakunan duniya duka suna nema su sadu da Sulemanu, don su ji irin hikimar da Allah ya ba shi.

24. Kowannensu yakan kawo masa kyautai na kayayyakin azurfa, da na zinariya, da riguna, da turare, da kayan yaji, da dawakai, da alfadarai, masu yawan gaske a kowace shekara.

25. Sulemanu kuwa yana da ɗakunan dawakai da na karusai dubu huɗu (4,000), yana da mahayan dawakai dubu goma sha biyu (12,000) waɗanda suke zaune a biranen karusai, waɗansu kuma a Urushalima tare da sarki.

26. Ya mallaki dukan sarakuna tun daga Yufiretis, har zuwa ƙasar Filistiyawa har kuma zuwa kan iyakar Masar.

27. Sarki ya sa azurfa ta gama gari, kamar duwatsu a Urushalima, ya kuma sa itatuwan al'ul su yalwata kamar itatuwan ɓaure a Shefela.

28. Dawakan Sulemanu, sayo su aka yi daga Masar, da dukan sauran ƙasashe.

29. Sauran ayyukan Sulemanu daga farko har ƙarshe an rubuta su a tarihin annabi Natan. An kuma rubuta su a annabcin Ahaija Bashilone, da kuma a wahayin Iddo maigani, game da Yerobowam ɗan Nebat.

Karanta cikakken babi 2 Tar 9