Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 9:15-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Sai Sulemanu sarki ya ƙera manyan garkuwoyi guda ɗari biyu na zinariya, kowace garkuwa nauyinta shekel ɗari shida ne na zinariya.

16. Ya kuma ƙera garkuwa ɗari uku ƙanana na zinariya, kowace garkuwa nauyinta shekel ɗari uku ne. Sarki fa ya ajiye su a gidan da aka gina da katakai daga Lebanon.

17. Sarki ya yi babban gadon sarauta na hauren giwa, ya dalaye shi da zinariya.

18. Gadon sarautar yana da matakai da 'yar kujerar zinariya ta ɗora ƙafa haɗe da gadon. A kowane gefen gadon an yi wurin ɗora hannu, akwai kuma siffar zaki a tsaye kusa da kowane wurin ɗora hannun.

19. Akwai kuma siffofin zaki goma sha biyu, zaki biyu a kowane mataki, gefe da gefe. Ba ma sarautar da aka taɓa yi irin wannan.

20. Dukan tasoshi da finjalai na sarki Sulemanu, da zinariya tsantsa aka yi su. Haka nan kuma dukan tasoshi da finjalai da suke cikin gidan da aka gina da katakai daga Lebanon, na zinariya ne tsantsa. Ba a mai da azurfa a bakin kome ba a zamanin Sulemanu.

21. Sau ɗaya a shekaru uku, sarki yakan aika da jiragen ruwa zuwa Tarshish tare da barorin Hiram, su kawo zinariya, da azurfa, da hauren giwa, da manyan birai, da ɗawisu.

22. Sarki Sulemanu ya fi dukan sarakunan duniya dukiya da hikima.

23. Sarakunan duniya duka suna nema su sadu da Sulemanu, don su ji irin hikimar da Allah ya ba shi.

24. Kowannensu yakan kawo masa kyautai na kayayyakin azurfa, da na zinariya, da riguna, da turare, da kayan yaji, da dawakai, da alfadarai, masu yawan gaske a kowace shekara.

25. Sulemanu kuwa yana da ɗakunan dawakai da na karusai dubu huɗu (4,000), yana da mahayan dawakai dubu goma sha biyu (12,000) waɗanda suke zaune a biranen karusai, waɗansu kuma a Urushalima tare da sarki.

26. Ya mallaki dukan sarakuna tun daga Yufiretis, har zuwa ƙasar Filistiyawa har kuma zuwa kan iyakar Masar.

Karanta cikakken babi 2 Tar 9