Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 6:4-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Sai ya ce, “Ubangiji Maɗaukaki ne, Allah na Isra'ila wanda ya yi wa tsohona Dawuda alkawari, ga shi kuwa ya cika shi, gama ya ce,

5. ‘Tun daga ranar da na fito da jama'ata daga ƙasar Masar, ban zaɓi wani birni daga cikin dukan kabilan Isra'ila ba, inda zan gina wurin da sunana zai kasance, ban kuma zaɓi wani mutum da zai shugabanci jama'ata Isra'ila ba.

6. Amma na zaɓi Urushalima domin sunana ya kasance a wurin, na kuma zaɓi Dawuda ya zama shugaban jama'ata Isra'ila.’

7. “Ya zama kuwa tsohona Dawuda ya yi niyyar gina Haikali domin sunan Ubangiji, Allah na Isra'ila.

8. Amma Ubangiji ya ce wa ubana Dawuda, ya kyauta, tun da yake ya yi niyya a zuciyarsa zai gina ɗaki saboda sunansa.

9. Duk da haka, ba shi zai gina Haikalin ba, ɗansa wanda za a haifa masa, shi ne zai gina Haikalin domin sunansa.

10. “Yanzu fa Ubangiji ya cika alkawarin da ya yi, gama na gāji matsayin ubana Dawuda, na kuwa hau gadon sarautar Isra'ila, yadda Ubangiji ya alkawarta, na kuwa gina Haikali domin sunan Ubangiji, Allah na Isra'ila.

11. A can na ajiye akwati inda aka sa alkawarin da Ubangiji ya yi wa jama'ar Isra'ila.”

12. Sulemanu ya miƙe a gaban bagaden Ubangiji a idon dukan taron Isra'ila ya ɗaga hannuwansa.

13. Sulemanu ya riga ya yi dakali na tagulla, tsawonsa kamu biyar, fāɗinsa kamu biyar, tsayinsa kamu uku, ya ajiye shi a tsakiyar filin, ya tsaya a kai. Ya durƙusa a gwiwoyinsa, a idon dukan taron jama'ar Isra'ila, ya ɗaga hannuwansa sama,

14. ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na Isra'ila, ba wani Allah kamarka a sama ko a duniya, wanda yake cika alkawari, kana nuna madawwamiyar ƙauna ga bayinka masu tafiya a gabanka da zuciya ɗaya.

15. Kai ka cika alkawarin da ka yi wa bawanka, tsohona Dawuda. Abin da ka faɗa ka kuma aikata.

16. Yanzu fa, ya Ubangiji, Allah na Isra'ila, ka cika alkawarin da ka yi wa bawanka tsohona cewa, ‘Daɗai, ba za a rasa wanda zai hau gadon sarautar Isra'ila ba, in dai 'ya'yanka maza za su lura da al'amuransu, don su yi tafiya bisa ga shari'ata, yadda kai ka yi tafiya a gabana.’

17. Saboda haka, ya Ubangiji, Allah na Isra'ila, ka tabbatar da maganarka wadda ka yi wa bawanka Dawuda.

18. “Ashe kuwa Allah zai zauna tare da ɗan adam a duniya? Ga shi kuwa, sama da saman sammai ba su iya ɗaukarka ba, balle fa ɗakin da na gina.

19. Duk da haka ka kula da addu'ar bawanka da roƙe-roƙensa. Ya Ubangiji Allahna, ka kasa kunne ga kuka da addu'ar da bawanka yake yi a gabanka.

20. Ka dubi wajen Haikalin nan dare da rana, wurin da ka yi alkawari za ka sa sunanka, ka kasa kunne ga addu'ar da bawanka zai yi wajen wannan wuri,

21. ka ji roƙe-roƙen bawanka da na jama'ar Isra'ila, sa'ad da suke addu'a suna fuskantar wannan wuri, ka ji daga wurin da kake zaune a Sama, sa'ad da ka ji, ka gafarta.

22. “Idan wani ya yi wa maƙwabcinsa laifi, har aka sa shi ya rantse, ya kuwa zo ya rantse a gaban bagaden a wannan Haikali,

23. sai ka ji ka yi wa bayinka shari'a daga Sama, ka hukunta wa mugun, ka ɗora masa alhakinsa, ka baratar da adalin, ka ba shi sakayyar adalcinsa.

Karanta cikakken babi 2 Tar 6