Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 35:12-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Sa'an nan suka keɓe hadayu na ƙonawa domin su rarraba bisa ga ƙungiyoyin gidajen kakanni waɗanda su ba firistoci ba ne, don su miƙa wa Ubangiji kamar yadda aka rubuta a littafin Musa. Haka nan kuma suka yi da bijiman.

13. Suka gasa ragon hadayar Idin Ƙetarewa bisa ga ka'idar, sai suka dafa tsarkakan hadayu a tukwane, da manyan tukwane, da kwanoni, nan da nan suka kai wa waɗanda ba firistoci ba.

14. Daga baya kuma suka shirya wa kansu da firistoci, saboda firistoci, 'ya'yan Haruna, maza, suna ta hidimar miƙa hadayu na ƙonawa, da kuma na kitse, har dare. Don haka Lawiyawa suka shirya wa kansu abinci, suka kuma shirya wa firistoci, 'ya'yan Haruna, maza.

15. Mawaƙa, 'ya'yan Asaf, maza, suna wurinsu bisa ga umarnin Dawuda, da Asaf, da Heman, da kuma Yedutun maigani na sarki, matsaran ƙofofi kuma suna a kowace ƙofa, ba lalle sai su bar wurin hidimarsu gama 'yan'uwansu Lawiyawa sun shirya musu nasu.

16. Haka fa aka shirya dukan hidimar Ubangiji a wannan rana, domin su kiyaye Idin Ƙetarewa, domin kuma su miƙa hadayu na ƙonawa a bisa bagaden Ubangiji, yadda Yosiya sarki ya umarta.

17. Jama'ar Isra'ila waɗanda suke wurin, suka kiyaye Idin Ƙetarewa, da kuma idin abinci marar yisti har kwana bakwai.

18. Ba a taɓa yin Idin Ƙetarewa irin wannan ba tun kwanakin annabi Sama'ila, ba wani kuma daga cikin sarakunan Isra'ila da ya kiyaye Idin Ƙetarewa kamar yadda Yosiya ya kiyaye shi tare da firistoci, da Lawiyawa, da dukan mutanen Yahuza da na Isra'ila, waɗanda suke a wurin, da kuma mazaunan Urushalima.

19. A shekara ta goma sha takwas ta mulkin Yosiya aka yi Idin Ƙetarewa.

20. Bayan wannan duka, sa'ad da Yosiya ya shirya Haikali, sai Neko Sarkin Masar, ya zo don ya yi yaƙi a Karkemish wadda take a Yufiretis, sai Yosiya ya fito don ya kara da shi.

Karanta cikakken babi 2 Tar 35