Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 26:5-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Ya mai da hankalinsa ga bin Ubangiji a kwanakin Zakariya, wanda ya koya masa tsoron Allah. Dukan lokacin da yake bin Ubangiji, Allah ya wadata shi.

6. Azariya kuwa ya tafi ya yi yaƙi da Filistiyawa, ya rushe garun Gat, da na Yamniya, da na Ashdod. Ya giggina birane a ƙasar Ashdod, da waɗansu wurare na Filistiyawa.

7. Allah ya taimake shi a kan Filistiyawa, da Larabawa, waɗanda suke zaune a Gur-ba'al, da kuma Me'uniyawa.

8. Ammonawa kuma suka kawo masa haraji, sunan Azariya ya kai har kan iyakar Masar, gama ya shahara ƙwarai.

9. Banda haka kuma, Azariya ya gina hasumiyai a Urushalima a Ƙofar Kusurwa, da Ƙofar Kwari, da kan kusurwa, ya kuma yi musu kagara.

10. Ya kuma gina hasumiyai a jeji, ya haƙa tafukka masu yawa, saboda yana da garkunan dabbobi da yawa, da waɗanda suke Shefela da waɗanda suke a filin tudu. Yana kuma da manoma da masu yi wa kurangar inabi aski a tuddai, da wajen ƙasashe masu dausayi, gama shi mai son noma ne ƙwarai.

11. Har yanzu kuma, Azariya yana da rundunar sojoji waɗanda suka iya yaƙi ƙungiya ƙungiya, yadda Yehiyel magatakarda, da Ma'aseya jarumi, suka karkasa su bisa ga umarnin Hananiya, ɗaya daga cikin 'yan majalisar sarki.

12. Jimillar shugabannin gidajen kakanni na ƙarfafan mutane jarumawa, dubu biyu da ɗari shida (2,600) ne.

13. Suna da sojoji dubu ɗari uku da dubu bakwai da ɗari biyar (307,500) a ƙarƙashin ikonsu waɗanda suke da ƙarfin yin yaƙi sosai, da za su taimaki sarki a kan maƙiyansa.

14. Azariya ya shirya wa sojojinsa garkuwoyi, da māsu, da kwalkwali, da sulke, da bakuna, da duwatsun majajjawa.

15. A Urushalima ya yi na'urori waɗanda gwanayen mutane ne suka ƙago don a sa su a hasumiya, da kan kusurwoyi, don a harba kibau, da manyan duwatsu. Da haka sunansa ya bazu ko'ina, gama ya sami taimako mai banmamaki, har ya zama mai ƙarfin gaske.

16. Amma sa'ad da ya yi ƙarfi, sai ya shiga girmankai, wanda ya zamar masa hallaka. Sai ya yi izgili a gaban Ubangiji Allahnsa, ya shiga Haikalin Ubangiji don ya ƙona turare a bisa bagaden ƙona turare.

17. Amma Azariya firist, ya bi shi tare da firistoci tamanin na Ubangiji, mutane ne jarumawa.

Karanta cikakken babi 2 Tar 26