Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 25:9-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Amaziya kuwa ya ce wa annabin Allah, “To, me za mu yi yanzu game da azurfar da muka ba sojojin Isra'ila?”Sai annabin Allah ya amsa ya ce, “Ubangiji yana da iko ya ba ka fiye da haka.”

10. Sai Amaziya ya sallami rundunar sojojin da suka zo daga Ifraimu, su koma gida. Sai suka yi fushi da Yahuza ƙwarai suka koma gida cike da hasala mai zafi.

11. Amma Amaziya ya yi ƙarfin hali ya shugabanci jama'arsa, suka tafi Kwarin Gishiri, suka karkashe mutanen Seyir dubu goma (10,000).

12. Mutanen Yahuza kuma suka kama waɗansu mutum dubu goma (10,000) da rai, suka kai su a ƙwanƙolin dutse, suka yi ta tunkuɗa su ƙasa daga ƙwanƙolin dutsen, duka suka yi kaca-kaca.

13. Amma sojojin rundunar da Amaziya ya sallama, bai yarda su tafi yaƙi tare da shi ba, suka faɗa wa biranen Yahuza da yaƙi, tun daga Samariya har zuwa Bet-horon, suka kashe mutum dubu uku (3,000), a cikinsu suka kwashe ganima mai yawan gaske.

14. Da Amaziya ya komo daga kisan Edomawa, sai ya kwaso gumakan mutanen Seyir, ya ajiye su su zama gumakansa, ya yi musu sujada, ya kuma miƙa musu hadaya.

15. Saboda haka Ubangiji ya yi fushi da Amaziya. Ubangiji ya aiki annabi a wurinsa. Annabin ya ce masa, “Don me ka koma ga gumakan da ba su iya ceton jama'arsu daga hannunka ba?”

16. Yana magana ke nan, sai sarki ya ce masa, “Yaushe muka naɗa ka mai ba sarki shawara? Ka rufe baki! In kuwa ba haka ba in sa a kashe ka.”Sai annabin ya yi shiru, amma ya ce, “Na dai sani Allah ya riga ya shirya zai hallaka ka, saboda ka aikata wannan, ba ka kuma saurari shawarata ba.”

17. Sa'an nan Amaziya Sarkin Yahuza, ya yi shawara ya aika wa Yehowash ɗan Yehowahaz ɗan Yehu, Sarkin Isra'ila, ya ce, “Ka zo mu gabza da juna fuska da fuska.”

18. Yehowash Sarkin Isra'ila fa ya aika wa Amaziya Sarkin Yahuza, da amsa ya ce, “Wata ƙaya ce a Lebanon, ta aika wa itacen al'ul na Lebanon cewa, ‘Ka ba ɗana 'yarka aure,’ sai wani naman jeji na Lebanon da yake wucewa, ya tattake ƙayar.

19. Ka ce, ga shi, ka ci Edom, zuciyarka ta sa ka fāriya. Amma yanzu sai ka yi zamanka, don me ka tsokano wahalar da za ta kā da kai, da kai da Yahuza tare da kai?”

Karanta cikakken babi 2 Tar 25