Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 24:11-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Duk lokacin da Lawiyawa suka kawo wa 'yan majalisar sarki babban akwatin sa'ad da suka gan shi cike da kuɗi, sai magatakardan sarki, da na'ibin babban firist, su zo su juye kuɗin da suke cikin babban akwatin, sa'an nan su mayar da shi a inda yake. Haka suka yi ta yi kullum, har suka tara kuɗi masu yawan gaske.

12. Sarki kuwa da Yehoyada suka ba da kuɗin ga waɗanda suke lura da aikin Haikalin Ubangiji. Suka sa magina, da masassaƙa su gyara Haikalin Ubangiji, suka kuma sa masu aikin baƙin ƙarfe da na tagulla su gyara Haikalin Ubangiji.

13. Sai ma'aikatan da aka sa su yi aikin, suka yi aiki sosai, suka tafiyar da gyaran, suka gyara Haikalin Ubangiji, ƙarfinsa ya koma kamar yadda yake dā.

14. Da suka gama aikin, sai suka kawo wa sarki da Yehoyada sauran kuɗin. Da waɗannan kuɗin aka yi tasoshi, da kayan girke-girke na Haikalin Ubangiji, da kuma kayan hidima da miƙa hadayu na ƙonawa, da tasoshi domin turare, da kwanoni na zinariya da na azurfa.Suka yi ta miƙa hadayu na ƙonawa a cikin Haikalin Ubangiji, dukan kwanakin Yehoyada.

15. Yehoyada kuwa ya tsufa ƙwarai, ya yi tsawon rai, ya rasu. Ya rasu yana da shekara ɗari da talatin da haihuwa.

16. Suka binne shi a birnin Dawuda a inda ake binne sarakuna, saboda ya aikata nagarta a Isra'ila, da kuma a gaban Allah da Haikalin Allah.

17. Bayan rasuwar Yehoyada, sai sarakunan Yahuza suka zo suka yi mubaya'a a gaban sarki, sarki kuwa ya karɓa.

18. Sai suka ƙyale Haikalin Ubangiji Allah na kakanninsu, suka bauta wa Ashtarot da gumaka. Hasala kuwa ta auko a kan Yahuza da Urushalima, saboda wannan mugunta da suka yi.

19. Duk da haka Allah ya aika musu da annabawa don su komo da su wurinsa. Ko da yake sun shaida musu kuskurensu, duk da haka ba su kula ba.

20. Sai Ruhun Allah ya sauko wa Zakariya, ɗan Yehoyada, firist, ya tsaya a gaban jama'a ya yi magana da su, ya ce, “Ga abin da Allah ya ce, ‘Don me kuke ƙetare umarnan Ubangiji, har da za ku rasa albarka? Saboda kun rabu da bin Ubangiji, shi ma ya rabu da ku.’ ”

Karanta cikakken babi 2 Tar 24