Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 20:1-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Bayan wannan sai mutanen Mowab, da mutanen Ammon, tare da waɗansu daga cikin Me'uniyawa, suka zo su yi yaƙi da Yehoshafat.

2. Sai waɗansu mutane suka zo suka faɗa wa Yehoshafat cewa, “Mutane masu yawan gaske suna zuwa su yi yaƙi da kai daga Edom, da kuma teku, har sun iso Hazazon-tamar,” wato En-gedi.

3. Sai Yehoshafat ya ji tsoro ya himmatu ga neman Ubangiji, ya kuma sa a yi shela, a yi azumi a dukan Yahuza.

4. Yahuza suka tattaru don su nemi taimako daga wurin Ubangiji. Daga cikin dukan biranen Yahuza, mutane suka zo don su nemi Ubangiji.

5. Sai Yehoshafat ya tsaya a gaban taron jama'ar Yahuza da na Urushalima, a Haikalin Ubangiji, a gaban sabuwar farfajiya,

6. ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na kakanninmu, kai ne Allah na cikin Sama, kai ne kuma kake mulkin dukan al'umman duniya. A gare ka iko da ƙarfi suke, don haka ba wanda ya isa ya jā da kai.

7. Ya Allahnmu, kai ne ka kori jama'ar ƙasan nan a gaban jama'arka Isra'ila, ka kuma ba da ita har abada ga zuriya masoyinka Ibrahim.

8. Suka kuwa zauna a cikinta, suka gina Wuri Mai Tsarki saboda sunanka cewa,

9. ‘Idan wani mugun abu ya same mu, kamar takobi, ko hukunci, ko annoba, ko yunwa, to, za mu tsaya a gaban wannan gida, a gabanka kuma, gama sunanka yana cikin gidan nan, idan mun yi maka kuka saboda wahalarmu, kai kuwa za ka ji, ka cece mu.’

10. “Yanzu kuma ga mutanen Ammon, da na Mowab, da na Dutsen Seyir, waɗanda ka hana Isra'ilawa su kai musu yaƙi sa'ad da suka fito daga ƙasar Masar, su ne mutanen da Isra'ila suka ƙyale, ba su hallaka su ba.

11. Dubi irin sakayyar da suka zo su yi mana, so suke su kore mu daga mallakarka, wanda ka gādar mana.

12. Ya Allahnmu, ba za ka hukunta su ba? Ba mu da ƙarfin da za mu yi yaƙi da wannan babban taro da suke zuwa su yi yaƙi da mu. Mun rasa abin da za mu yi, amma a gare ka muke zuba ido.”

13. A sa'an nan kuwa mutanen Yahuza suna tsaye a gaban Ubangiji, su da ƙananansu, da matansu, da 'ya'yansu.

Karanta cikakken babi 2 Tar 20