Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 2:5-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Haikalin nan kuwa da nake niyyar ginawa babba ne, gama Allahnmu ya fi dukan alloli.

6. Amma wa ya isa ya gina masa Haikali, shi wanda sama da saman sammai ba su iya ɗaukarsa ba. Ni wane ne da zan gina masa Haikali, sai dai wurin da za a riƙa ƙona turare a gabansa?

7. Saboda haka sai ka aiko mini da mutum wanda ya gwanance a kan aiki da azurfa, da tagulla, da baƙin ƙarfe, da kuma shunayya, da garura, da shuɗɗan zare, da wanda kuma ya gwanance da aikin sassaƙa, domin ya yi aiki tare da gwanayen mutane da nake da su a Yahuza da Urushalima, waɗanda tsohona Dawuda ya kawo.

8. Ka kuma aiko mini da itacen al'ul, da na fir, da katakon algum daga Lebanon, gama na sani barorinka sun san yadda ake yanyanka katakan Lebanon. Barorina za su yi aiki tare da barorinka,

9. domin su shirya mini katako mai yawa. Gama Haikalin da zan gina mai girma ne ƙwarai, mai banmamaki.

10. Zan ba barorinka masu aikin katako misalin mudu dubu ashirin (20,000) ta sussukakkiyar alkama, da mudu dubu ashirin (20,000) ta sha'ir, da misalin garwar ruwan inabi dubu ashirin (20,000), da ta mai dubu ashirin (20,000).”

11. Hiram, Sarkin Taya kuwa, ya ba Sulemanu amsar takardarsa, ya ce, “Saboda Ubangiji yana ƙaunar jama'arsa, ya naɗa ka sarkinsu.”

12. Hiram ya ci gaba da cewa, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Isra'ila, wanda ya yi sama da ƙasa, ya ba sarki Dawuda ɗa mai hikima, mai hankali, mai ganewa, wanda zai gina Haikali dominsa, ya gina fāda kuma domin kansa.

13. Yanzu zan aika maka da Huram mutum mai gwaninta, mai ganewa.

14. Shi ɗan wata mace mutuniyar Dan, mahaifinsa kuwa mutumin Taya ne. Huram ya gwanance a kan aiki da zinariya, da azurfa, da tagulla, da baƙin ƙarfe, da dutse, da itace, da kuma shuɗi, da shunayya, da garura, da lilin mai kyau. Shi kuma zai iya sassaƙa kowane irin abu da aka sa shi ya sassaƙa, tare da gwanayenka, da na tsohonka, ubangidana, wato Dawuda.

15. To, yanzu, sai ka aiko wa barorinka da alkama, da sha'ir, da mai, da ruwan inabi kamar yadda ka alkawarta.

16. Mu kuwa za mu yanko maka dukan katakan da kake bukata a Lebanon, mu kawo maka su a kan gadajen fito ta hanyar teku, zuwa Yafa, domin ka kwashe ka kai Urushalima.”

17. Sarki Sulemanu ya ƙidaya dukan baƙin da suke a ƙasar Isra'ila, kamar yadda tsohonsa Dawuda ya yi. Yawan baƙin da aka samu sun kai dubu ɗari da dubu hamsin da uku, da ɗari shida (153,600).

Karanta cikakken babi 2 Tar 2