Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 16:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A shekara ta talatin da shida ta mulkin Asa, sai Ba'asha, Sarkin Isra'ila, ya haura ya fāɗa wa Yahuza da yaƙi, ya gina Rama don ya hana kowa fita, ko shiga wurin Asa, Sarkin Yahuza.

2. Sa'an nan Asa ya ɗebo azurfa da zinariya daga dukiyar da take cikin Haikalin, da na fādar sarki, ya aika wa Ben-hadad da su, wato Sarkin Suriya, wanda yake zaune a Dimashƙu, yana cewa,

3. “Bari mu haɗa kai, da ni da kai kamar yadda ubana da naka suka yi. Ga shi, na aika maka da azurfa da zinariya. Ka tafi ka warware haɗa kan da yake tsakaninka da Ba'asha, Sarkin Isra'ila, don ya janye ya rabu da ni.”

Karanta cikakken babi 2 Tar 16