Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24
  25. 25
  26. 26
  27. 27
  28. 28
  29. 29
  30. 30
  31. 31
  32. 32
  33. 33
  34. 34
  35. 35
  36. 36

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Kabilan Arewa sun yi Tawaye

1. Rehobowam ya tafi Shekem, gama dukan Isra'ilawa sun tafi don su naɗa shi sarki.

2. Da Yerobowam ɗan Nebat, ya ji wannan labari (gama a Masar yake sa'ad da ya guje wa sarki Sulemanu), Yerobowam kuwa ya komo daga Masar.

3. Aka aika a kira shi, sai Yerobowam da dukan Isra'ilawa, suka je wurin Rehobowam suka ce,

4. “Tsohonka ya tsananta mana, yanzu sai ka sawwaƙa mana irin tsananin da muka sha daga wurin tsohonka, da irin tilastawar da ya yi mana, sa'an nan sai mu bauta maka.”

5. Rehobowam kuwa ya ce musu, “Ku komo bayan kwana uku.” Sai jama'a suka tafi.

6. Rehobowam ya nemi shawara a gun dattawan da suke tare da tsohonsa Sulemanu, sa'ad da yake da rai, ya ce, “Wace shawara za ku ba ni don in amsa wa jama'ar nan?”

7. Su kuwa suka ce masa, “Idan za ka nuna wa jama'ar nan alheri, ka daɗaɗa musu rai, ka kuma yi musu magana mai daɗi, za su zama barorinka har abada.”

8. Amma ya ƙi yarda da shawarar da dattawan suka ba shi, ya nemi shawara daga wurin matasa waɗanda suka girma tare, masu yi masa hidima.

9. Ya ce musu, “Wace irin shawara za ku bayar wadda za mu amsa wa jama'an nan da suka ce mini, ‘Ka sawwaƙa mana wahalar da muka sha daga wurin tsohonka’?”

10. Sai matasa waɗanda suka girma tare da shi, suka ce masa, “Ga abin da za ka faɗa wa jama'an nan da suka ce maka, tsohonka ya tsananta musu, yanzu sai ka sawwaƙa musu, ‘Ƙaramin yatsana ya fi ƙugun ubana kauri!

11. Ubana ya tsananta muku ƙwarai, amma ni zan tsananta muku fiye da shi, ubana ya hore ku da bulala, amma ni zan hore ku da kunamai.’ ”

12. Sai Yerobowam tare da dukan jama'a suka koma wurin Rehobowam a rana ta uku, kamar yadda sarki ya faɗa, “Bayan kwana uku ku komo.”

13. Sarki Rehobowam ya amsa musu da kakkausan harshe, gama bai karɓi shawarar dattawan ba.

14. Sarki Rehobowam ya yi aiki da shawarar da matasa suka ba shi, ya ce, “Ubana ya tsananta muku fiye da shi, ya hore ku da bulala, amma ni, da kunama zan hore ku.”

15. Sarki bai kasa kunne ga jama'ar ba, gama wannan al'amari, Allah ne ya aukar da shi, domin ya cika maganar da ya faɗa wa Yerobowam ɗan Nebat, ta bakin Ahaija Bashilone.

16. Da Isra'ilawa duka suka ga sarki bai saurare su ba, jama'ar kuwa suka amsa wa sarkin, suka ce, “Wane rabo muke da shi a wurin Dawuda? Ba mu da gādo a wurin ɗan Yesse. Kowa ya tafi alfarwarsa, ya ku Isra'ilawa. Ku bar Rehobowam ya lura da gidansa.”Isra'ilawa duka kowa ya tafi alfarwarsa.

17. Amma Rehobowam ya ci gaba da mulki bisa Isra'ilawan da suke a biranen Yahuza.

18. Sai sarki Rehobowam ya aiki Adoniram shugaban aikin dole, jama'ar Isra'ila kuwa suka jejjefe shi da duwatsu har ya mutu. Sai sarki Rehobowam ya gaggauta ya hau karusarsa, ya tsere zuwa Urushalima.

19. Tun daga wannan lokaci kuwa har zuwa yau, Isra'ilawa suka tayar wa gidan Dawuda.