Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 8:7-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Elisha kuwa ya tafi Dimashƙu. A lokacin kuwa Ben-hadad, Sarkin Suriya, yana ciwo. Aka faɗa masa cewa, annabi Elisha ya zo, yana nan,

8. sai sarki ya ce wa Hazayel, ɗaya daga cikin fādawansa, “Ka ɗauki kyauta, ka tafi wurin annabin Allah ka sa ya roƙar mini Ubangiji ko zan warke daga wannan cuta.”

9. Hazayel kuwa ya tafi wurin Elisha tare da kyauta iri iri na kayan Dimashƙu. Raƙuma arba'in ne suka ɗauko kayan. Da ya tafi ya tsaya a gabansa, ya ce, “Danka, Ben-hadad Sarkin Suriyawa, ya aiko ni wurinka don yana so ya ji ko zai warke daga wannan cuta.”

10. Elisha kuwa ya ce masa, “Tafi ka faɗa masa zai warke, amma Ubangiji ya nuna mini lalle zai mutu.”

11. Sai Elisha ya kafa wa Hazayel ido, yana kallonsa, har Hazayel ya ji kunya. Elisha kuwa ya fashe da kuka.

12. Hazayel ya ce, “Me ya sa shugabana yake kuka?”Elisha ya amsa ya ce, “Domin na san irin muguntar da za ka yi wa jama'ar Isra'ila. Za ka ƙone kagaransu da wuta, ka karkashe samarinsu da takobi, za ka kuma fyaffyaɗe ƙananansu a ƙasa, ka tsattsage matansu masu ciki.”

13. Hazayel kuwa ya ce, “Ni wane ne? Ina na sami wannan iko? Ni ba kome ba ne.”Elisha ya amsa ya ce, “Ubangiji ya nuna mini za ka zama Sarkin Suriya.”

14. Sa'an nan Hazayel ya tashi daga wurin Elisha ya koma wurin Ben-hadad. Ben-hadad ya tambaye shi, “Me Elisha ya faɗa maka?”Sai ya ce, “Ya faɗa mini, cewa lalle za ka warke.”

15. Amma kashegari sai Hazayel ya ɗauki bargo, ya tsoma a ruwa, sa'an nan ya rufe fuskar sarki da shi har ya mutu.Sai ya hau gadon sarautarsa.

16. A shekara ta biyar ta sarautar Yehoram ɗan Ahab Sarkin Isra'ila, Yoram ɗan Yehoshafat Sarkin Yahuza, ya ci sarauta.

17. Yana da shekara talatin da biyu da haihuwa sa'ad da ya ci sarautar. Ya yi shekara takwas yana sarauta a Urushalima.

Karanta cikakken babi 2 Sar 8