Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 7:10-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Sai suka tafi wurin masu gadin ƙofar birnin, suka ce musu, “Mun tafi sansanin Suriyawa ba mu ga kowa ba, ba mu kuma ji motsin kowa a wurin ba, ba kowa a wurin sai dawakai da jakai, a ɗaure, alfarwai kuma suna nan yadda suke.”

11. Sa'an nan masu tsaron ƙofar birnin suka aika a faɗa a gidan sarki.

12. Sai sarki ya tashi da dare ya ce wa fādawansa, “Bari in faɗa muku irin shirin da Suriyawa suka yi a kanmu. Sun sani muna fama da yunwa, domin haka suka fita daga sansanin suka ɓuya a karkara, suna nufin sa'ad da muka fita daga birnin, sai su kama mu da rai, sa'an nan su shiga birnin.”

13. Ɗaya daga cikin fādawan sarki ya ce, “A sa waɗansu mutane su ɗauki dawakai biyar da suka ragu cikin birnin, idan ba su tsira ba, za su zama kamar sauran Isra'ilawan da suka riga suka mutu. Bari mu aika, mu gani.”

14. Aka ɗibi mahayan dawakai biyu, sarki kuwa ya aike su, su bi bayan sojojin Suriyawa, ya ce musu, “Ku tafi, ku gani.”

15. Sai suka bi bayansu har zuwa Kogin Urdun, suka ga tufafi da makamai barjat ko'ina a hanya, waɗanda Suriyawa suka zubar lokacin da suke gudu. Sai manzannin suka komo suka faɗa wa sarki.

16. Sa'an nan mutane suka fita, suka washe sansanin Suriyawa. Aka kuwa sayar da mudu na lallausan gari da mudu biyu na sha'ir a bakin shekel ɗaya ɗaya kamar dai yadda Ubangiji ya faɗa.

17. Sarki kuwa ya sa dogari wanda ya raka shi wajen Elisha ya tsare ƙofar birnin. Sai mutane suka tattake shi a ƙofar har ya mutu, kamar yadda annabi Elisha ya faɗa sa'ad da sarki ya tafi wurinsa.

18. Ya faru daidai yadda annabi Elisha ya ce wa sarki, “Za a sayar da mudu biyu na sha'ir, da mudu na lallausan gari a bakin shekel ɗaya ɗaya gobe war haka a ƙofar birnin Samariya.”

19. Dogarin ya ce wa Elisha, “Ko da Ubangiji da kansa zai buɗe tagogin sama, wannan abu zai yiwu ke nan?”Elisha kuwa ya ce, “Za ka gani da idanunka amma ba za ka ci ba.”

20. Haka kuwa ya zama gama mutane suka tattake shi a ƙofar har ya mutu.

Karanta cikakken babi 2 Sar 7