Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 4:6-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Da tandayen suka cika ta ce wa ɗanta, “Kawo mini wani tandu.”Ɗan kuwa ya ce mata, “Ai, ba saura.” Sai man ya janye.

7. Sai ta koma ta faɗa wa annabi Elisha, shi kuwa ya ce mata, “Ki je ki sayar da man, ki biya bashin, abin da ya ragu kuwa ki ci, ke da 'ya'yanki.”

8. Wata rana Elisha ya wuce zuwa Shunem inda wata mace take da zama, sai ta gayyace shi cin abinci. Don haka duk lokacin da ya bi ta wannan hanya, sai ya ratsa ta gidanta, ya ci abinci.

9. Sai ta ce wa mijinta, “Na gane wannan mutum adali ne, mutumin Allah, wanda kullum yakan wuce ta hanyan nan.

10. Bari mu gina masa ɗan ɗaki a kan bene, mu sa masa gado, da tebur, da kujera, da fitila, don duk sa'ad da ya zo ya sauka a wurin.”

11. Wata rana da Elisha ya zo, ya shiga ɗakin, ya huta.

12. Sai ya ce wa baransa, Gehazi, “Kirawo matan nan.” Da ya kirawo ta, sai ta zo ta tsaya a gabansa.

13. Ya ce wa Gehazi, “Ka tambaye ta me take so in yi mata saboda dukan wannan wahala da ta yi dominmu? Tana so in yi mata magana da sarki ko da shugaban sojoji?”Sai ta ce, “Ai, ina da dukan abin da nake bukata a cikin jama'ata.”

14. Elisha ya ce, “To, me za a yi mata?”Sai Gehazi ya amsa ya ce, “Ai, ba ta da ɗa, mijinta kuwa tsoho ne.”

15. Sai ya ce, “Kirawo ta.” Da ya kirawo ta, sai ta zo ta tsaya a ƙofar ɗakin.

16. Elisha kuwa ya ce mata, “Baɗi war haka za ki rungumi ɗa na kanki.”Sai ta ce, “A'a, ya shugabana, mutumin Allah, kada fa ka yi mini ƙarya.”

Karanta cikakken babi 2 Sar 4