Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 20:12-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. A lokacin nan sai Merodak-baladan, ɗan Baladan, Sarkin Babila, ya ji labarin rashin lafiyar Hezekiya, sai ya aiki manzanni da wasiƙa da kyautai su kai wa Hezekiya,

13. Hezekiya kuwa ya marabce su, ya kuma nuna musu dukan taskokin dukiyarsa na azurfa, da na zinariya, da na turare, da na mai mai daraja, da na makaman yaƙinsa, da dukan abin da yake akwai a cikin ɗakunan ajiyarsa. Ba abin da ya rage daga cikin gidansa, ko a mulkinsa wanda bai nuna musu ba.

14. Sai annabi Ishaya ya tafi wurin sarki Hezekiya ya ce masa, “Daga ina ne waɗannan mutane? Me suka ce maka?”Hezekiya ya amsa, ya ce, “Sun zo daga ƙasa mai nisa, wato Babila.”

15. Ishaya ya ce, “Me suka gani a fādarka?”Hezekiya ya ce, “Sun ga duk abin da yake ciki, ba wani abu kuma daga cikin taskokina da ban nuna musu ba.”

16. Sa'an nan Ishaya ya ce wa Hezekiya, “Ka ji abin da Ubangiji ya ce,

17. ‘Lokaci yana zuwa da za a kwashe duk abin da yake cikin gidanka, da abin da kakanninka suka tanada, zuwa Babila.

18. Za a kuma kwashe waɗansu 'ya'yanka da ka haifa zuwa Babila, can za a maishe su babani a fādar Sarkin Babila.’ ”

19. Sarki Hezekiya kuwa ya fahimci za a yi zaman lafiya da salama a zamaninsa, don haka ya amsa ya ce, “Jawabin da ka kawo mini daga wurin Ubangiji yana da kyau.”

20. Sauran ayyukan Hezekiya da dukan ƙarfinsa, da yadda ya yi tafki da wuriyar ruwa don ya kawo ruwa cikin birnin, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.

21. Hezekiya kuwa ya rasu. Sai ɗansa, Manassa, ya gāji gadon sarautarsa.

Karanta cikakken babi 2 Sar 20